ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa A Daminar Da Ta Gabata Masara Ta Yi Tsada -Shugaba

by Abubakar Abba
2 years ago
Masara

Har yanzu noman Masara a kasar nan, musamman a arewa maso yamma suna yin noman ta da tsadar gaske.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar manoman Masara don samun riba na yankin arewa maso yamma Alhaji Adamu Muhammad Makarfi ya sanar da cewa, a kakar noman bana.

  • GORON SALLAH
  • Amsar Xi Jinping Ta Ba Duniya Damar Fahimtar Tsarin Binciken Hada-hadar Kudin Na Kasar Sin

Har yanzu noman Masara a kasar nan, musamman a arewa maso yamma suna yin noman ta da tsadar gaske.

ADVERTISEMENT

Adamu a hirarsa da Leadership Hausa a kaduna yace, sabin yadda ake sayar da takin kan naira 5,000 a baya, a bana farashinsa ya ninka, inda ya ce, hatta  magungunan feshi na kwari ko na kashe Ciyawa da kudin kwadago, kudaden su sun karu.

Ya ci gaba da cewa, haka ambaliyar ruwan sama  da aka samu a wasu jihohin kasar nan kamar su, Zamfara, Sokoto, Jigawa, Katsina kaduna da wasu jihohin duk an samu wannan iftila’in, inda hakan ya janyo wa manoma yin asara.

LABARAI MASU NASABA

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

Ya kara da cewa,  “ A matsayi na, na manomi mu bukatar mu ba  wai a sayar da amfanin gona da tsada a kasar nan ba, amma duk da haka, ba za mu so ace manoma sun yi asara ba, domin asarar manoma, asara ce ga kasa baki daya”.

Ya yi nuni da cewa,  domin duk ida aka ce manomi ya yi noma kuma ya fadi, babban abinda ake jin tsaro, musamman manyan manoma da yawancin su suke yin noman don riba in sun fadi akwai matsala domin akasarin suna ciwo bashi ne a banki domin yin noma da kuma kudin ruwan da ake dora masu, asarar za ta yi masu yawa.

Adamu ya ci gaba da cewa, idan manyan manoma ba su yi noma ba a kasar nan, za samu karancin abinci, inda ya ce, hakan ne ya sa zaka ga ana yin kira aje a sawo abinci daga ketare, in an sawo abincin daga ketare, Nijeriya za ta iya yin asara mai yawa domin hakan zai iya dfurkusar da tattalin arzikin kasar nan.

Ya yi nuni da cewa, misali an je an sawo tan miliyan biyu  na Masara don shigo wa da shi cikin Nijeriya, sai an kashe kusan naira tiriliyan daya, inda ya kara da cewa, a kasar  nan ,  ban da sauran amfanin gona  kasar nan na bukatar akalla tan miliyan ashirin.

Ya ce, in har za a sawo Masara a kasar waje ba a noma a kasar nan ba, akalla za  mu yi asarar  zunzurutun kudi kamar naira tirilyan goma, inda ya yi nuni da cewa, idan ba a baiwa manoman kasar taimakon da ya dace, ba karamar matsala ce za ta auku ba.

Ya yi  kira  musamman  ga gwamnatin tarayya, gwamnatin jihohi da na kananan hukumomi su mayar da hankali kan bunkasa noman rani, inda ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi a samar da kyakyawan tsari, amma idan ba  a yi hakan ba, bamu san irin abinda zai faru a kasar nan ba.

Da yake yin tsaokaci kan tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi na dakile ‘yan kasuwa na kasar waje zuwa gonakan manoman kasar nan don sayen amfanin gona da suka noma kai tsaye, Makarfi ya ce, wannan tsarina bin yaba wa ne, sai ya sanar da  gwamnatin ta makaro domin tun tuni ya kamata ace an yi irin wannan tsarin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Noma Da Kiwo

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi
Noma Da Kiwo

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
Noma Da Kiwo

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

November 2, 2025
Next Post
Muhimmancin Kafa Cibiyar Kulawa Da Lafiyar Hakori

Muhimmancin Kafa Cibiyar Kulawa Da Lafiyar Hakori

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

November 14, 2025
ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

November 14, 2025

Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar

November 14, 2025
Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G

Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G

November 14, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 14, 2025
Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

November 14, 2025
Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

November 14, 2025
Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

November 14, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

November 14, 2025
Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe

Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.