Jama’a barkanku da Juma’a barkanku da kasance wa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A. Shafin da ke baku damar mika sakon gaishe-gaishenku zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki, na kusa da na nesa. Kafin na je ga sakonnin da nake tafe da su sai na fara mika sakon gaisuwa ta musamman zuwa ga Editana Abdulrazak Yahuza Jere da fatan zai yi juma’a lafiya. Sakon goron juma’a ga ‘Yan uwa da abokan arziki na kusa dana nesa duk ina yi muku fatan alkhairi. Yanzu kuma zan bude kadan daga cikin sakonnin masu karatu kamar haka:
Sako daga Fadila Aliyu Musa Jihar Kano:
Ina gaida ‘yan uwana wato Aliyu Musa Kamaran Family, ina gaida yarana Aisha Faizu Musa, Yasmin Faizu, ina gaida dukkanin daukacin al’ummar musulmi baki daya.
Sako daga Safna Aliyu Jawabi:
Ina mika sakon gaisuwa ga habibina (Heart owner) kawata Husaina Sani, sahibar raina Nusaiba Nuhu, Sadiya Ahmad Sulaiman (SAS) Yayata Aunty Mairo my Little Safnah.
Sako daga Hafsatu Yusuf Garin Kano unguwar Gadon Kaya:
Da farko ina gaida ni kaina Hafsat Yusuf Muhd (ummi), Gadon kaya ina gaida kawuna engineer ruwasa Ibrahim gamji dake garin marke Jigawa, ina gaida yayyena Sani Yusuf da kuma Salisu Yusuf da Saratu Yusuf. Sai kuma kanne na Hauwa’u Yusuf da Aisha Yusuf da Khadija Yusuf Zahra’u Yusuf, Abdurrashi Yusuf. Babbar gaisuwata ina gaida mahaifiyata Hajiya Maryam da mahaifina Yusuf Muhd, sannan ina gaida masoyina Ibrahim Idris Koki gaisuwa maitarin yawa.
Sako daga Pretty Deeje Jamhuriyar Nijer:
ina gaida my babbar Yaya, babbar kawata, aminiyata, kuma kawar Tsokanata My Rabiat.
Sako daga Hadi Tsohon Sarki Daura 08164205067:
Assalam gaisuwar goron juma’a ga mai girma Nut ciyaman na daura da mal. Lawal da mai girma mataimakin sakatare Nut Daura Mal. Habu Popula da sabon ciyaman na Nut ta jahar katsina dan kafin Daura Allah ya taya shi riko, da fatan sun yi Juma’a lafiya.
Sako daga Zahra’u Abubakar (Dr Zara) Jihar Kano Nassarawa LGA Gama-D:
Ina mika sakon barka da juma’a na a gareka Ibrahim Muhammad (Abban Ruma) kana da matsayi sosai a zuciyata shiyasa na zabi mika maka sakon gaisuwata a wannan shafin tare a cikin jaridar Leadership kuma Kai kadai Tak!, na rasa kalmomin da zan tattara in fadi irin yadda nake jin ka a cikin zuciya ta, mutum na farko wanda ba zan iya mantawa da shi ba a wannan bangaren jajirtacce akan dukkanin lamura na kalmar nan da hausawa suke cewa shi da ba a san iya wanda yake cin albarkacinsa ba akan ka ne na gaskata ya rabbi ka ginawa mahaifiyar wannan bawa naka gida a Aljannar firddausi da iyayen mu baki daya Allah ya kara mata Lafiya Allah ya faranta mata ya jibanci dukkanin lamuranta.
Sako daga Maryam Abdullahi Jihar Kano:
Ina gaida Khadija Sa’id, Fatima, Amina, Aisha, Zainab, Safiyya, Sajida, Rukayya da khadija kabir da fatan suna nan lafiya.