Gidauniyar Bunkasa Fannin Aikin Noma (NADF), ta kulla yarjejeniyar da Bankin Manoma na Kasa da kuma kungiyar kasa da kasa ta bunkasa kasuwanci (IDH), musamman domin sama wa matasa da mata kudaden yin noma.
Har ila yau, za a sama musu da kudaden ne, domin yin noman Rogo da samun riba a karkashin shirin sana’o’i na WISE. An rattaba hannun yarjejeniyar ne, a yayin kaddamar da shirin na WISE a Jihar Legas, inda kaddamarwar ta nuna irin matakai da dabarun da aka dauka na karfafa samar da kudade ga matasa da kuma matan da ake so su amfana.
- Tinubu Da Shugabannin ECOWAS Sun Gudanar Da Taron Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau
- Sin Ta Kasance Mai Goyon Bayan Kasashen Afirka Wajen Zamanantar Da Kansu
Babban Jami’i a kungiyar IDH, Daan Wensing, a jawabinsa a wajen rattaba hannun yarjejeniyar, wani mataki ne na samar da kudaden yin noma da kuma tabbatar da dorewar fannin.”Gaza samun kudaden yin noman, ya kasance tamkar wani gibi ne da ke jawo dakatar da matasa daga samun damar shiga fannin yin noma, domin samun riba; amma a yanzu muna kokarin samar da wani sabon tsari da zai taimaka musu wajen samun kudaden shiga, domin yin noman Rogo don samun riba,” in ji Jami’in.
Shi ma, a nasa jawabin a wajen yarjejeniyar, Manajan Darakta a Bankin Manoma, Ayodeji Sotinrin, ya bayar da tabbacin bankin na ci gaba da bunkasa fannin aikin noma a kasar.”Daga cikin ayyukanmu a bankin, sun hada da samar wa da manoma kudaden yin noma, musamman a bangaren yin noma, domin samun riba.” a cewarsa.
Ya kara da cewa, wannan yarjejeniyar, za ta taimaka wajen karfafa samar da kudaden yin noma da kara samar da wadataccen abinci a kasar da kuma kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar.
Haka zalika, shi ma shugaban sashen zuba hannun jari a gidauniyar ta NADF, Abdullahi Imam, wanda ya wakilci sakataren kashe kudade na gidauniyar ya bayyana cewa; hadakar a tsakanin abokan hadakar na da matukar mahimmanci.














