Abdulrazak Yahuza Jere" />

Abin Da Ya Sa Ingila Gaskata Zaben Nijeriya

Gwamnatin Kasar Ingila ta tabbatar da cewa sakamakon zaben shugaban kasa da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana na gaskiya ne.
Ministar kasar mai kula da hulda da Afirka, Harriett t Baldwin wadda ta bayyana haka, ta yi bayanin cewa hujjarsu ta sahihantar sakamakon zaben shi ne “ya yi dai-dai da wanda wata kungiya mai zaman kanta (Parallel Bote Tabulation Process) da ta yi nazarin zaben ta ayyana.”
“Tare da sauran kawayenmu na duniya, Ingila ta yi amannar cewa ‘Yan Nijeriya za su iya samun gamsuwa da sakamakon zaben,” in ji ta.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Yakubu ne ya ayyana sakamakon zaben da goshin asubahin ranar Larabar nan, inda ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zaben ranar 23 ga Fabrairun 2019, da kuri’a Milyan 15 da dubu 191, da dari 847. Inda babban mai kalubalantarsa, Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP, ya samu kuri’a milyan 11 da dubu 262 da dari 978. Sai dai wakilin PDP a cibiyar tattara sakamakon zaben ya ki rattaba hannu a takardar sakamakon zaben, kana daga bisani Atiku shi ma ya shure sakamakon, ya ce bai yarda ba kuma zai garzaya kotu.
Minista Baldwin ta taya Shugaba Buhari murnar samun wa’adin mulkinsa na biyu inda ta ce, “Ina taya Shugaba Buhari murna a kan samun wa’adin mulkinsa na biyu a matsayin shugaban Nijeriya,” kamar yadda ta bayyana a sanarwar da Ofishin Jakadancin Ingila da ke Nijeriya ya fitar a Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ingila da Nijeriya sun jima suna kawance da juna kuma tana hada kai da Nijeriya da mutanen kasar domin samar da cigaba a Nijeriyar da kuma duniya baki daya.”
Har ila yau, ta yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka riga mu gidan gaskiya a hatsaniyar zaben. Tana mai cewar “Bai dace wani ya mutu a kokarinsa na amfani da ‘yancin da dimukuradiyya ta bashi ba.”
Baldwin ta yaba wa ‘Yan Nijeriya saboda jajircewarsu da kuma kukewa ga tsarin dimukuradiyya.
Sai dai kuma, ta tabo batun koke-koken da wasu ‘Yan Nijeriyan suka yi game da tsarin zaben, musamman wurin matakan gudanar da zaben da tattara sakamako da kuma rahotannin yi wa malaman zabe barazana da ba su gwale-gwale a wasu wuraren.
Ministar ta yi kira ga duk wani mai korafi da yake so ya kalubalanci zaben, ya yi hakan cikin lumana kuma ta hanyar da shari’a ta amince.
“Muna karfafa gwiwar mahukuntan Nijeriya su binciki zarge-zargen da aka yi na aikata ba dai-dai ba cikin tsanaki kuma su dauki kwararan matakan da suka dace a kan wadanda suka yi laifukan,” in ji sanarwar.
Daga bisani, Ministar ta jaddada goyon bayan da Ingila za ta cigaba da baiwa Nijeriya da kungiyoyinta na taimakon al’umma, “bisa darassun da kasar ta samu a wannan zaben da kuma karfafa tsarinta na mulkin dimukuradiyya,” in ji ta.

Exit mobile version