Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta sayo takin zamani da aka dauko a cikin manyan motoci sama da 200, domin raba wa al’ummar jihar a matsayin daya daga cikin matakan bayar da tallafi.
Mutfwang ya bayyana hakan ne a garin Jos; babban birnin jihar a lokacin da ya kai ziyarar aiki, domin duba takin zamani da ke tashar jiragen sojin sama a garin na Jos.
- Cutar Anthrax: Yadda Masu Kiwon Dobbobi Suka Shiga Zullumi A Jos
- Gidauniyar TY Buratai Ta Nemi ‘Yan Nijeriya Su Kara Hakuri Da Salon Mulkin Tinubu
Gwamnan ya ci gaba da cewa, babbar manufar samar da takin shi ne, domin samar da dauki tare da amfanin gona, musamman don a kara samar da wadataccen abinci a Jihar Filato da kuma matikin kasa baki-daya.
Bugu da kari ya bayyana cewa, kyakkyawan shiri na nan tafe ta yadda za a raba wannan taki na zamani, domin tabbatar da ganin ya isa ga wadanda ake so su amfana kai tsaye.
A cewarsa, “Muna so mu sanar da cewa, tuni mun bayar da umarnin shigo da manyan motoci 200 na takin zamani, wadanda a halin yanzu tuni an riga an dauko su”, in ji shi.
Gwamnan ya kara da cewa, muna kammala shirye-shiryen rabar da takin, za mu tura shi zuwa ga kananan hukumomi 17 na jihar.
Kazalika gwamna Mutfwang ya bayyana muhimmancin yin amfani da takin wajen yin noma, amma ba kuma wai domin wadanda ake so su amfana da shi su karkata akalarsa wajen sayar da shi, don biya bukatun kashin kansu ba.
Sannan gwamnan ya kuma jaddada kokarin da gwamnatinsa ke yi na kara bunkasa fannin aikin noma a jihar ta Filato, musamman domin bai wa fannin taimakon da ya kamata domin amfanin al’umma baki-daya.
A nasa jawabin, Babban Sakataren Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Filato (PLASEMA), Hon. Sunday Abdu ya sanar da cewa, sama da manyan motoci 170 dauke da takin zamani aka sauke tare da jiran karin wasu manyan motoci 40 nan gaba.