Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta bayyana dalilin da ya sa ta tsare Mista Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, a ranar Litinin.
Dakta Peter Afunanya, kakakin DSS ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
- NUC Ta Daga Darajar Kwalejin Ilimi Ta Sa’adatu Zuwa Jami’ar Ilimi Ta Kano
- Shugabar Matan NNPP Reshen Abuja Ta ‘Yanta Fursunoni 4
Afunanya ya ce sun gudanar da wani bincike ne da ya shafi wasu zarge-zarge da batancin da tsohon ministan ya yi kan batutuwan da suka shafi tsaron kasa.
Ya ce an sa Fani-Kayode ya fuskanci tambayoyi kan furuncinsa na cewar ana shirin aikata juyin mulki a kasar nan.
Ya ce an umarci tsohon ministan da ya rika kai ziyara ofishin hukumar DSS daga ranar Laraba har zuwa lokacin da za a kammala binciken a kan sa.
Afunanya ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su yi taka-tsan-tsan wajen yin furucin da ka iya haifar da rikici gabanin babban zabe.
Ya bukaci mutane da su kaucewa furta kalaman da ba su da cikakkiyar hujja a kai.
A ranar Litinin ne DSS ta gayyaci Fani-Kayode inda ta tsare amma daga bisani ta bayar da belinsa.