Abin Da Ya Sa Na Ke Son Zama Gwamnan Jihar Gombe -Inuwa Yahaya

Alhaji Inuwa Yahaya Umaru na xaya daga cikin ‘yan siyasar da suka nuna aniyarsu na zama gwamnan jihar Gombe ta qarqashin jam’iyyar APC, a tattaunawarsa da Wakilinmu Bello Hamza a babban ofishinsa dake Abuja ya yi bayanin irin tanadi da tsare tsaren daya shirya wa al’ummar jihar Gombe don bunqasa rayuwarsu, ga dai yadda tattaunawar ta kasance.
Za mu so sanin suna da kuma taqaitaccen tarihinka.
Sunana Muhammadu Inuwa Yahaya Umaru. Ni mutumin Gombe ne. An haifeni a cikin garin Gombe. Shekaruna 58 a duniya. Ni a halin yanzu xan kasuwa ne. Sannan ina yin hada-hadar siyasa. Na shiga siyasa sosai ne lokacin da aka dawo mulkin dimokraxiyya a shekarar 1999, wato lokacin mulkin shugaba Obasanjo. A wancan lokaci ian cikin jam’iyyar PDP.
Bayan an kafa gwamnati a shekarar 2003, in da Alhaji Muhammadu Xanjuma Goje ya zama Gwamna a jihar Gombe, ya xaukoni ya ba ni kwamishinan kuxi a jihar Gombe. To a nan ne na daxa shiga cikin siyasa sosai.
To ina nan a matsayin kwamishinan kuxi har zuwa shekarar 2010, in da na bar muqamin kwamishinan kuxi. A wannan lokacin na so na yi takarar Gwamna amma Allah bai yarda ba. Daga baya na koma jam’iyyar CPC, muka ci gaba da tafiya har zuwa shekarar 2014, in da na tsaya takarar Gwamna. Ni na yi wa jam’iyyar APC takarar kujerar Gwamna a jihar Gombe a wannan shekara. Wato bayan an yi haxaka kenan inda aka koma jam’iyyar APC. Amma Allah bai yarda ba, saboda haka ban zama gwamna ba a wannan lokaci. Kuma insha Allahu har yanzu ina da niyyar yin takarar Gwamna a cikin jam’iyyar APC a zaven da ke tafe a shekarar 2019.
Yallavai ka yi takarar Gwamna a shekarar 2011 da kuma 2015, yanzu kuma kana son sake yin takara a shekarar 2019. Me ya ja hankalinka har kake son ka zama Gwamna a jihar Gombe?
Akwai abubuwa da dama da nake son yi wa al’ummar jihar Gombe amma babba daga cikinsu shi ne lokacin da na yi kwamishinan kuxi na ga abubuwa da dama da ya kamata a yi don jama’a su fita daga cikin mawuyacin halin da suke ciki. Sannan mu’amulata da mutane da fuskar kasuwanci na san dabaru kala-kala da al’umma za ta amfana da su ta fuskar ci gaba. Kuma ina ganin ina da dabaru da kuma qwarewa da zan yi amfani da su don fitar da mutanenmu daga cikin halin talauci da kuma qunci.
Wani abu da ke xaukar hankali yanzu shi ne yadda ake ficewa daga jam’iyyarku ta APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP. Ba ka ganin wannan abu zai iya kawo maka cikas a qoqarinka na zama Gwamnan jihar Gombe?
Bana zaton haka, saboda waxanda suka fita ba su kai waxanda suka shigo martaba da kwarjini ba a siyasa. Saboda haka ba wata barazana da muke fuskanta. Domin yawancin waxanda suka fita mun tantancesu lokacin zaven shugabannin jam’iyya da aka yi. Saboda suna kawo mana rashin zaman lafiya da tsegumi a cikin jam’iyya. Don haka ficewarsu daga cikin jam’iyyar qarfi zai qara mana sosai domin muna tare da jama’a kuma jama’ar ne suka kawo jam’iyyar APC. Saboda haka muna da tabbacin insha Allahu za mu kafa Gwamnati a jihar Gombe.
Jihar Gombe na xaya daga cikin jihohin da suka fito daga yankin arewa maso gabashin qasar nan. Wato yankin da ya yi fama da rikicin Boko Haram, talauci da kuma rashin aikin yi. A matsayinka na tsohon kwamishinan kuxi ko akwai wani shiri da kake da shi don farfaxo da tattalin arzikin jihar Gombe?
Lallai hakan na xaya daga cikin dalilin da ya sa na ke son zama gwamnan jihar Gombe, domin ni matsanin tattalin arziki ne, kuma xan kasuwa ne, sannan manoni ne. Zan iya ce maka ma kusan gado na yi. Don haka na goge a cikin harkar noma da kasuwanci sosai. Na san matsalolin manoma kamar yadda na san matsalolin ‘yan kasuwa. Jihohinmu na arewacin qasar nan gaba xaya kashi 85 na al’ummarmu manoma ne. Idan aka tsaya tsakani da Allah aka gyara vangaren harkokin noma al’ummarmu za ta amfana sosai. Suma masu dakon amfanin gona xin za su sami nasu amfanin. Sannan suma kamfanonin da ke sarrafa amfanin gonar suma za su sami ci gaba sosai. Kai har ma ‘yan kasuwa za su amfana sosai, Domin abin hannun dama ne ya wanke na hagu.
Jihar Gombe na xaya daga cikin jihohin da ke fama da ‘yan saka-suka, wato waxanda ake kira da suna ‘yan kalare. Idan ka zama Gwamnan jihar Gombe wane mataki za ka xauka don magance wannan barazana?
Alhamdulillahi duk wanda ya san tafiya ya san bana son ta’addanci. Kamar yadda ba zan so xa na ya yi ta’addanci ba, haka ba zan so xan wani ya yi ba. Saboda haka dole za mu zauna da iyaye mu haxa hannu mu xauki matakan da za su kawo qarshen kowane irin ta’addanci. Mu fito da hanyoyi da waxannan matasa za su faxaka su gane. Dole mu kuma nema musu sana’ar da za su yi don dogaro da kai. Saboda haka ina ganin idan har aka sa himma kuma aka yi tsakani da Allah, ba za a xauki lokaci mai tsawo ba za a shawo kan wannan matsala.
Wane kira kake da shi ga al’umma don ganin sun ci gaba da baiwa shugaba Muhammadu Buhari goyon baya da kuma sake zavensa a zaven da ke tafe a shekarar 2019?
Ni masoyin shugaba Muhammadu Buhari ne, masoyin jam’iyyar APC ne. Kuma masoyin kawo canji ne don al’ummarmu su sami jin daxi da walwala. Tsarin mulki irin na dimokraxiyya ya nuna cewa kowane zango na shekaru huxu sai an sake gudanar da zave. Saboda haka ina jira ga jama’a da su ci gaba da baiwa Shugaba Muhammadu Buhari goyon baya, domin ya gwada mana cewa matsalolin da suka damemu zai iya magance mana su. Saboda ya cika mana wasu daidai gwargwado fiye da waxanda suka yi mulkin a bayansa. Domin su suka fatattaka tsarin tsaronmu, suka sanyamu cikin ruxu da damuwa. To yanzu al’amura sun fara komawa daidai. Don haka muna fatan idan aka sake ba shi dama zai yi bakin qoqarinsa wajen daidaita al’amura. Shima muna yi masa fatan zai xauki mutanen masu kirki da kuma son jama’a don tallafawa Gwamnatinsa ta cika alqawuran da ta yi wa al’umma.
Wane saqo kake da shi ga al’umma musamman na jihar Gombe?
To saqona ga al’umma musamman na jihar Gombe, domin ni xan jihar ne, shi ne mu zauna lafiya da juna. Domin zaman lafiya ne kaxai zai iya kawo man duk abin da muke buqata na ci gaba. Kuma al’amari ne da yake buqatar haxin kan kowa da kowa. Ko ina a duniya sai an sami fahimtar juna da zaman lafiya sannan ake samun ci gaba.
Yallavai mun gode qwarai da gaske
Nima Na gode

Exit mobile version