Daya daga cikin matasa masu goyon bayan Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP, ya bayyana dalilinsa na yin tattaki matukar dan takarar ya lashe zaben 2023. Ga tattaunawarsa da Rabi’at Sidi Bala kamar haka:
 Ya sunanka?
Sunana Aminu Hassan haifaffen garin Suleja dake Jihar Neja.
Me za ka ce game da siyasar 2023?
Ni dan Jamiyyar PDP ne, na yi kudurin in sha Allahu rabbi, in Allah ya ba Alhaji Atiku Abubakar nasarar lashe zaben 2023 zan yi tattaki daga Jihar Neja zuwa Abuja.
Me ya sa za ka yi tattakin?
Abun da ya janyo hankalina wajen yin wannan tattaki shi ne; tunda na taso har zuwa girmana ban da wani dan siyasa wada ya wuce Alhaji Atiku Abubakar.
Ko akwai wata boyayyiyar alaka tsakaninka da shi ne?
Gaskiya ba ni da wata halaka da Alh
Atiku Abubakar kuma asali ma ban taba ganinsa ba, kuma ba jiharmu daya da shi ba, kawai cancantar sa ce ma ta sa nayi kudurin haka.
Ba ka tunanin irin kallon da sauran al’umma za su yi maka, musamman ganin yadda kusan hakan ya faru ga wasu a lokutan baya?
Eh! Na san mutane da dama za su yi kallon wahalalle wanda bai da aikin yi, duk abun da za su ce bai dame ni ba, kawai na yi wannan tsakani da Allah, da ya halince ni.
Ya kake kallon yadda jam’iyyar za ta kasance wajen samun nasarar lashe zabe?
Eh! Kin san muliki na Allah ne, amma ina yin kyankyawan zato, akwai nasara. Amma a gun Allah yake Allah bamu, in ba mu kasa ya zama mafi alheri a gare mu baki daya.
Wanne sako kake da shi ga al’umma baki daya?
Eh! to sako da al’ummar Nijeriya shi ne; Allah ya zaba mana shugaba mafi alheri a gare mu baki daya. Sannan su tabbarta sun zabi Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban Nijeriya na 2023, saboda shi ne ya fi cancanta, shi kuma ya san matsala Nijeria saboda, na san ina masa fatan Allah ba shi sa’a da nasara duk wanda ya nufe shi Allah ka sa ya zama alkhairi a gare shi, alfarmar Annabi Muhammad (SAW).