Connect with us

LABARAI

Abin Da Za A Yi Da Dala Miliyan 320 Da Abacha Ya Sata -Buhari

Published

on

wamnatin tarayya ta bayyana cewa, za ta kashe dala milyan 320 da Abacha ya sata kan wani shiri na musamman mai suna, ‘Conditional Cash Transfer scheme,’ wanda zai amfani talakawa, a ranar Litinin ne gwamnatin ta bayyana hakan a Abuja.

Da yake bude taro na takwas na cibiyoyin yaki da cin hanci da rashawa a  Afrika na kasashen renon Ingila, Buhari, wanda mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya wakilce shi, ya ce hakan yana daga cikin sharadin da gwamnatin kasar Switzerland ta bayar kafin ta yarda ta dawo da kudin.

Buhari ya ce, Kungiyar kwato dukiyoyin da aka sace ta duniya, (GFAR), ce bayan an kaddamar da ita a birnin Washington, a watan Disamba 2017, ta shirya yanda hanyar ganowa da kwato kudin za ta kasance.

“Daga cikin sharadin da aka gindaya kan dawo wa da kudin shi ne za a zuba kudin ne cikin wani shiri na musamman, wanda zai amfani talakawa ne kadai.

Buhari, ya bayyana cewa matsalar cin hanci da rashawa yana daga cikin kalubalen da ke fuskantar nahiyar Afrika, sai ya yi kira da hadin kan kasashen duniya wajen kawar da shi.

Ya bayar da misalin rahoton wata kungiya mai taken, “Satan dala triliyon daya,” wanda ta fitar a shekarar 2014, inda kungiyar ta yi zargin cewa kasashe masu tasowa suna asarar dala bilyan daya a duk shekara, mafi yawa ga kamfanonin bogi.

Hakanan ya kara yin tilawar wani rahoton da ya fito a shekarar 2015, daga wata babbar cibiya mai binciken karakainan kudi daga kasashen Afrika, wacce tsohon Shugaban kasan Afrika ta kudu, Thabo Mbeki, ke shugabanta, wacce ta bayyana cewa, Afrika ta yi asarar sama da dala triliyon daya cikin shekaru 50.

Rahoton ya kara da cewa, Afrika ta yi asarar sama da dala bilyan 50 a duk shekara kan karakainan kudi yawanci ga kamfanonin bogi da ba wanda ya san tahakikanin masu su.

“Ruguza hanyar hada baki da ke kai ga satan dukiyoyi yana da mahimmanci tamkar dai taken wannan taron na, “Hada kai domin dawo da dukiyoyin da aka sace.”

“Kwato wa da dawo da dukiyoyin da aka sace ba kawai amfanin sa dawo wa da dukiyoyin ne ba, ya kan ma zama darasi ga masu nufin yin satan a gaba.”

Buhari ya koka da rashin dokokin hana cin hanci da rasahawa a wasu kasashen, da bambancin shari’u da tsare-tsare, matsalan bambancin harshe, boye sirruka na Bankuna, matsalolin shari’a, a matsayin ababen da ke kawo tarnaki a yakin da ake yi.

Buhari ya bukaci kasashen Afrika da su hada kai wajen mahimmantar da batun na ganowa da kwato dukiyoyin da aka sace, su kuma yi kokarin gina gada mai karfi tsakanin su da sauran kasashen duniya ta fahimtar juna.

“Dole ne mu tabbatar da an dawo da dukkanin dukiyoyin da aka sace zuwa kasashen su na asali, ba tare da gindaya wani sharadi ba kamar yanda yake a doka ta 51 kan cin hanci da rashawa ta Majalisar Dinkin Duniya.”

Ya kuma kirayi kasashen na Afrika da su dauki nauyin hukumomin su masu yaki da cin hancin da rasahawa yadda ya kamata, a cewar sa, yakin da cin hanci da rashawa babbar matsala ne fiye da tunanin su, sannan fiye da yadda lamarin yake a

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: