Rabiu Ali Indabawa" />

Abincin Biki Ya Yi Ajalin Mutum 2, 17 Na Kwance A Asibiti A Katsina

Mutane biyu ne suka riga mu gidan gaskiya, yayin da wasu 17 ke kwance a asibiti suna karbar magani bayan sun ci abincin da ake zargin akwai guba a cikinsa a wani gidan biki a Katsina. Mutane biyun da suka mutu, Bilkisu Surajo mai shekaru 2O da Ibrahim Sani mai shekaru 13 duk ‘yan kasar jamhuriyar Nijar ne da ke makwabtaka da Katsina.
Mai magana da yawun ‘yan Sandan jihar, S. Gambo Isah ya ce tuni an damke wasu mutane biyu da ake zarginsu da sanya gubar cikin abincin.
Rahoton da ‘Yan Sanda suka rubuta ya ce wani matashi mai shekaru 25, Musa Suleiman ne ya hada baki da wata Shafa’atu Sujaro inda suka saka Zakami a cikin abincin da za a ba wa ‘yan biki.
Dukkansu biyu suna zaune ne a gida daya da ke kauyen Ali Yaba da ke yankin Mani a jihar ta Katsina.
Tuni dai an kama su kuma sun amsa cewa sun saka Zakamin cikin abincin bikin. Wani takaitaccen vidiyon da ‘Yan Sanda suka fitar, ya nuna Shafa’atu tana amsa cewa Musa ya bata shinkafa da ruwa a bokiti domin ta dafa abincin da baki za su ci. Musa shi ma ya amsa cewa ya bata kayayyakin amma bai bayyana dalilin da ya sa ya ba ta ba. Kazalika, a ranar 7 da 9 ga watan Afrilun 2O2O tsakanin karfe 12 na dare da 5 na asubahi, ‘Yan Sandan ‘Operation uff adder’ sun dakile wani hari da barayin shanu suka kai kauyukan Dan Alhaji da Zamfarawa. Sun kama wani Abubakar Maiunguwa Alti mai shekaru 26 da ke zaune a rugar Fulani na Dogon Dutsen Akata a garin Batsari na jihar Katsina inda suka kwato shanu a hannunsa.
Alti ya yi kaurin suna wurin ta’addanci kuma ya amsa cewa yana daga cikin wadanda suka kai hare-hare a kauyukan Batsari duk dai a jihar ta Katsina.

Exit mobile version