Shugaban Kungiyar Matasan Kwankwasiyya na Kasa (Kwankwasiyya National Youth Congress, KNYC), Nasir Isah Garun Malam, ya bayyana cewar abubuwan da suka faru game da harin da aka kai wa mabiyar darikar siyasar Kwankwasiyya yayin Hawan Daushe a Birnin Kano, alamu ne da suke nuna gazawar gwamnati mai ci a fili. A cewarsa, duk wani mutum da ya san tsarin siyasar ci gaban al’umma, bai za goyi bayan irin wannan sare-sare da sunan bambancin siyasa ba.
Nasir Garun Malam ya fadi haka ne a wani taron manema labarai da Kungiyar ta shirya a Birnin Abuja, inda ya ce sam abubuwan da suka faru sun sabawa tsarin siyasar ci gaban kasa da al’ummarta.
Ya ce, hakika su ‘yan Kwankwasiyya ba su ji dadin abinda ya faru ba, kuma hakan alamun nasara ne ga tafiyarsu ta Kwankwasiyya, a cewarsa magoya bayan Gandujiyya sun kara haskawa duniya cewar ba za su iya tabuka wani abu a siyasance ba sai ta hanyar sara da suka.
“Wadanda suka aikata wannan abu sam ba ‘yan siyasa ba ne, ‘yan jagaliya ne kawai. Wadanda suke fushi da fushin wani. A matsayin Jihar Kano na alkiblar siyasar Nijeriya, bai dace irin wadannan abubuwa su rika faruwa ba.” In ji shi.
“Shugabanninmu da wannan abu ya rutsa da su masu hankali ne, shi ya sa ba su yi wata magana a kai ba, wanda na tabbatar su tsagin wadanda suka yi wannan abu ba haka suka so. Bukatarsu a yi kare-jini-biri-jini. Sai suka yi rashin sa’a, tuni Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gama zuba madarar hankali a kwakwalen matasan Jihar Kano musamman mabiya Kwankwasiyya.
Ya ce, karon farko kenan a tarihin siyasa da irin haka ta taba faruwa, inda wasu gungun jama’a da suke ikirarin goyon bayan Gwamnati, za su dauki makami su rufarwa wani bangaren na ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi sanadin hayewar jagoransu kan karagar mulki, ciki da har tsohon Sakataren Gwamnati da kuma kani ga tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.
“A tarihin Kano, Kwankwaso ne Gwamna na farko da ya hana daba ta hanyar yin amfani da ilmi; ya samarwa da matasa ayyukan a fanni daban-daban, wadanda ko makiyinsa ya sani. Matasa sun shagaltu da ayyukan ci gaba a wancan lokaci, saboda haka babu mai tunanin daukar makami ya farwa wani da sunan siyasa.
Nasir Isah ya kuma yi kira ga matasa da su daina bari ana amfani da su wajen jagaliyanci, domin a karshe babu wanda zai cutu sai su.
A karshe ya yi wa wadanda balahirar ta shafa addu’ar samun sauki tare da jinjina gare su bisa juriyarsu da suka na rashin mayar da martini. Inda ya ce lokaci na zuwa wanda mabiya darikar Kwankwasiyya za su rama a akwatunan zabe.