Abokan Hamayyar Kungiyoyin Asiri Sun Yi Arangama A Jihar Abiya

Kungiyar Asiri

Daga Rabiu Ali Indabawa

An kashe mutum uku yayin da wasu kungiyoyin asiri biyu da ke gaba da juna suka yi artabu a Aba, Jihar Abia. Jaridar The Nation ta tattaro cewa, rikicin na karshen mako tsakanin kungiyoyin Aye da Aro ya kasance ne saboda fifikon babban birnin kasuwanci na jihar. An bayar da rahoton kashe mutum biyu a yankin Omuma da ke Ama-Ogbonna, yayin da gawar mamaci na uku ya tsinke a kan hanyar Aba-Owerri.

Wadansu sun kira wannan mako da suna ‘karshen mako na jini’ a cikin garin kasuwanci. Kungiyoyin tsafi na Aye da Aro, manyan mutane biyu da suka shahara a Aba, sun kasance a makogwaron juna cikin ‘yan watannin da suka gabata. Wannan jarida ta ruwaito kwanan nan cewa an kashe wani mutum mai shirin komawa malesiya a baya a wata mashahuriyar hanyar Ngwa.

Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, kisan na da nasaba da kishiyar kungiyoyin asiri, wani abu da ya samo asali tun bayan takaita zirga-zirga. Majiyar ta ce an kama da yawa daga wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne tare da gurfanar da su a gaban kotuna daban-daban, kuma wasu an tura su zuwa gidan yarin da ke Aba da Umuahia, babban birnin jihar.

Majiyar ta tabbatar da mutuwar mutanen ukun, ta kara da cewa babu wani rahoto a hukumance game da kisan, sannan ta kara da cewa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suna aiki tukuru don dakile ayyukan kungiyar asiri a cikin garin. Majiyar ta gargadi iyaye da su zama masu lura da abokan da ‘ya’yansu ke rike da su da kuma kayan da su ke kawowa gida.

Wasu kayayyaki da yara su ka zo gida da su na iya zama mallakar wani dan kungiyar asiri da a ka kashe, in ji shi.

“Abin da wasunsu ke yi shi ne amfani da wayar wani dan kungiyar asiri da suka kashe don yaudarar wasu ‘yan kungiyar asirin zuwa wurin da za su kashe su su ma.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa iyaye da masu kula su yi tambayoyi lokacin da suka ga abubuwan da ba su saya wa ‘ya’yansu sun kawo gida. “Yana da matukar damuwa a yanzu, musamman a wannan lokacin da tsofaffi ke daukar yara hatta daliban firamare cikin kungiyar tsafinsu.”

Exit mobile version