Tun bayan da kasar Sin ta kaddamar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, tattalin arzikin kasar ta fara kama hanyar samun ci gaba cikin sauri. Saboda haka manufar gyare-gyare na da ma’ana mai muhammanci ga kasar.
A kwanan baya, kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake rike da ragamar mulki a kasar, ya gudanar da cikakken zaman taronsa na uku, inda aka tsara manufofi masu alaka da tattalin arziki da sauran harkokin mulki, da za a aiwatar da su cikin shekaru fiye da 10 masu zuwa, kana an zartas da kudurin kara zurfafa gyare-gyare, da ingiza aikin zamanantar da kasa ta dabarar musamman ta kasar Sin.
- Zanga-Zanga Ko Kun San Babban Dalilin Garƙame Abusalma A Kurkuku
- Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba: Nijeriya Na Asarar Naira Biliyan 9 Duk Shekara – Majalisa
Wannan taro ya nuna dorewar manufofin kasar Sin. A ko da yaushe kasar tana nacewa ga bin hanyar da ta dace da yanayin da take ciki. Kana idan mun kwatanta manufofin da kasar Sin ta gabatar a wajen taron na wannan karo da tarukan da suka gudana a baya, za mu ga yadda kasar ta gaji manufofi na baya, gami da kokarin raya su a kai a kai.
Abu na biyu da taron ya nuna mana shi ne ra’ayin shugabannin kasar Sin na kokarin daukar hakikanan matakai, inda idan an gamu da matsala, to, sai a yi kokarin daidaita ta hanyar yin gyare-gyare. A wajen taron jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin na wannan karo, an gabatar da matakan gyare-gyare fiye da 300, wadanda a cikinsu akwai matakan da aka tsara bisa inganta wasu tsoffin matakai, gami da wasu sabbin matakan da aka kirkira don biyan bukatun daidaita wasu sabbin matsalolin da ake fuskantar. Sa’an nan matakan kasar Sin na daidaita manufofi da yin gyare-gyare sun nuna amfaninsu, har ma sun samu amincewa daga kafofin watsa labaru na Najeriya. Misali, jaridar the Guardians ta kasar Najeriya ta wallafa wani bayani a shafinta ta yanar gizo ta Internet, wanda ya yi kira da a koyi dabarar kasar Sin ta rage talauci. An ce, ta hanyar yi wa tattalin arziki gyare-gyare, da kai dauki ga iyalai masu fama da talauci yadda suke bukata, kasar Sin ta fitar da jama’arta fiye da miliyan 800 daga kangin talauci, adadin da ya kai kashi 75% na al’ummar da aka fid da su daga kangin talauci a duk duniya.
Sa’an nan abu na 3 da wannan taro ya nuna shi ne, maimakon gabatar da manufofi yadda ta ga dama, kasar Sin ta tsara manufofinta ne bayan gudanar da nazari da tattaunawa cikin wani dogon lokaci. Hakika wasu watanni kafin budewar taron na wannan karo, Xi Jinping, babban magatakardan kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya jagoranci wani taron sauraron ra’ayin kwararru na sassa daban daban, dangane da aikin kula da harkokin kasa, inda ya jaddada bukatar sauraron ra’ayin jama’a bisa abubuwan da suke bukata, da shawarwarin da za su iya gabatarwa, don tabbatar da samar da daidaitattun manufofi.
To, mene ne muhimmancin taron da ya gudana a kasar Sin a wannan karo, ga kasar Najeriya, da sauran kasashen dake nahiyar Afirka?
Da farko, yadda kasar Sin ta tsara manufofi bisa wani daidaitaccen tsari, da kokarin aiwatar da su yadda ake bukata, ya nuna cewa, kasar wata abokiyar hulda ce da ake iya hadin gwiwa da ita cikin dogon lokaci da wani yanayi mai karko. Duk wani matakin da kasar Sin ta dauka, ta tsara shi ne bisa gudanar da bincike na dogon lokaci, da yin tattaunawa tsakanin mutanen sassa daban daban. Saboda haka, babu bukatar damuwa kan rashin dorewar manufofinta, kuma da wuya ne a samu wata manufar da aka tsara cikin kuskure, yayin da ake hadin gwiwa da Sin.
Na biyu shi ne, yadda kasar Sin take kokarin zurfafa gyare-gyare da zamanantar da al’ummarta shi ma zai daga matsayin hadin gwiwarta da Najeriya, gami da sauran kasashen dake nahiyar Afirka baki daya.
Misali, a wajen taron jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin na wannan karo, an gabatar da manufofi na kara bude kofa ga kasashen waje, da kyautata tsarin aiwatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, da tabbatar da daidaito tsakanin mabambantan kasashe, da dunkule tattalin arzikin duniya waje guda a kokarin tabbatar da moriyar kowace kasa, da dai makamantansu.
Idan an kwatanta da kisan gillar da aka nema yi wa Donald Trump a baya bayan nan, wanda ke takarar neman zama shugaban kasar Amurka, da sauran ayyukan siyasa na kasar Amurka, masu cike da karfin tuwo da tashin hankali, taron da ya gudana a kasar Sin a wannan karo, da sauran ayyukan siyasa na kasar, tamkar “babu gishiri” a cikinsu.
Amma yayin da ake neman abokan hulda, ba za a nemi “masu gishiri” ba, maimakon haka, an fi son zabar abokai da suka san ya kamata, wadanda ke iya daukar hakikanan matakai masu amfani cikin natsuwa. (Bello Wang)