Daga Hussaini Baba
Sarkin Noma na Kasa Alhaji Hassan Muhammad Kwazo Gusau ya bayyana cewa’ Abubuwa uku da ba a sa Siyasa a cikinsu su ne, tsaro da kiwon Lafiya da Kuma noma. Sarkin ya bayyna haka ne a lokacin da ya ke zanta wa da Leadershi A Yau a ofishinsa da ke Gusau.
Basaraken ya bayyana cewa ‘ Abu na Farko shi ne tsaro, a harkar tsaro bai kamata a sa siyasa ba don haka, gwamnatin tarayya ta ki yarda da yin ‘yan sandan jihohi, da zarar an yi su siyasa za ta shiga ciki kuma haka da akai ya yi daidai, shibne mafitar wannan al’uma da kasa baki daya .Abu na biyu kuwa shine kiwon Lafiya,shima bai kamata ba Gwamnatocin falle uku ,Gwamnatin tarayya da jahohi da Kannan hukumamomi su sa Siyasa a ban garen Lafiya ba dan sanya Siyasa a sashen lafiya ba zai haifar da da mai ido ba.dan haka ma wsu jahohin su kan fita Kasashen waje dan naimo Likitoci dan ceto rayukan alumma.Abuna uku shine Noma.Noma shine ginshikin Rayuwar alumma.samar da a Abinci ga gwamnati wajibi ne ta samar wa alumma abinci,kuma abincin bai samuwa sai ta hanyar Noma dan haka shi Noma shine ke rike da Duniya lafiya dan duk kasar da ke da yinwa babu zama lafiya dan haka sanya siyasa a Harkar Noma babu abubda zai harfar sai Yinwa a kasa da asarar Rayuka.
A lokacin da Gwamnatin Tarayya tace zata bada tallafin Noma ta hannun Babban Bankin Kasa muka bada shawara da cewa ‘Gwamnati ta bar Ma’aikaatr Gona da wannan shirin tallafawa manoma da kudin yin Noma dan itace tasan hakikanin manomi da inda ya ke da inda gonarsa ta ke,sai banki Kasa yace duk mai san bashi Noma yaje yayi rijista a bashi bashi yayi Noma kin baiwa Ma’aikatar Gona aikin ta Akasa siyasa a ciki gashi da yawa Manoma na gaskiya basu amfana da wannan tallafin ba.
Sarkin Noma ya kuma kara da cewa ‘Abinci fa shine rayuwar alumma dan ko yaki ake sai anci abunci ballatana zaman lafiya.dan haka siyasar da ake sawa aharkar Noma a kasar nan lallai ba zai harma da da mai idoba.
Dan haka nake kira ga gwamnatin tarayya da ta maida Harkar noma gaba dayanta ga Ma’aikatar Gona,ita tasan suwaye Manoma na gaskiya,kuma sanya Sarakunan Noma da Hakimai a cikin shirin zai taimaka wajan ganin kwaliya ta biya kudin sabulu.
Kuma jinkirin ba Manomi tallafi yana jawo nakasu wajan samun amfanin Gona .misali idan gwamnati zata bada tallafin Noman Rani ya kamata ta bada shi a cikin watan Shada zuwa watan daya na sabuwar shekara idan Manomi ya samun wannan tallafi a cikin wannan lokaci sai ya samu amfanin da bai taba tsammani ba.amma idan aka samu sabani Allah ya sawake abun sai dai adu’a.batun Noman Damuna ya kamata idan gwamnati zata bada talfain Noman Damuna ya kamata ta bada shi a cikin watan biyu zuwa tawan uku Manomi ya samu kayan aikin da wuri dan haka zayyi iyaka kokarisa na ganin ya faar aiki akan lokaci kuma amfanin da zai samu sai ya ba kuwa maamki amma jinkirin bata tallafi da Takin Zamni acikin farashi mai sauki,sai guri ya kure na Rani na Damuna kuwa sai Ruwa ya dade da zuba a badashi to allai idan akai haka ba’ayi niyar taimawa manomi ba idan anasan taimakwan manomi abashi tallafi da wuri .ina mai shedawa Gwamnati cewa idan akaba Manomi tallafi da wuri kasar nan sai mun noma abunda zai riketa kuma ta dogara da shi da yardar Allah.