Abubuwan Da Ke Janyo Mutuwar Aure A Kasar Hausa

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Hausa na cikin manyan harsunan Nijeriya da ma Afirika musamman ta yamma, kuma harkar aure a wajen Malam Bahaushe kan burge jama’a bisa wasu al’adun musamman yadda Addinin Musulunci ya yi kane-kane a ciki.

Haka ya sa auren diyar Bahaushe ya fi araha kan auren wasu kabilun a Nijeriya, musamman kafin bayyanar wasu al’adun da aka aro daga wasu kabilu daban daban Matakan aure a Kasar Hausa guda 6 ne:

  1. Na gani ina-so Watau matakin farko kenan da zarar saurayi ya ga tsaleliyar Budurwar da yake so daga nan sai ya nemi amincewar iyaye domin jarraba sa’ar sa. A nan ne ake fara binciken addini da nasaba da kuma dabi’ar juna.
  2. Soyayya – Daga nan idan an dace sai ka ga an fara kulla alaka har ta kai ga soyayya, ana kara kuma fahimtar juna idan abu ya gyaru sai ka ji an kai ga tambaya.
  3. Kayan Gaisuwa- Bayan an yi zance iya zance sai dangin namiji su fara kai gaisuwa wajen dangin matar, ana mika kayan gaisuwa irin su tufafi da kudi, wanda da zarar an karba sai a fara maganar sadaki.
  4. Sadaki – A addinin Musulunci yawanci sadakin ‘ya mace ba ya kasa da rubu’in dinari, watau daya cikin hudu na farashin kilo na gwal. Idan akwai wadata kuma iya kudin ka iya shagalinka! Amarya ta kan sha kwalliya domin bikin aure.
  5. Sa rana – Da ance an amince da kudin sadaki sai kuma a sa ranar daura aure, Saurayi zai nemi gidan da za a tare yayin da dangin mace ke kawata gidan.
  6. Daurin aure da walima- Shi kenan kuma sai Allah ya kawo ranar daurin aure, inda a marya za ta ci kunshi da duk wata kwalliyar Duniya shi kuma Miji ko wakilin sa a daura masa aure da matar sa.

Bayan nan sai ayi addu’o’in da za ayi da kuma ‘yar walima domin a ci kuma a sha, a karshe sai a kai amarya gidan mijin ta!

Ko shakka babu idan aka dubi wadannan matakai za’a tabbatar da cewa tuni aka yi fatali da su aka aro wasu al’adun da halin yanzu ke neman zame mana kadangaren bakin tulu, Musamman shigar karya da kuma son ace auren wane ake ko wance. Manyan abubuwan da suka gurbata wasu kyawawan al’adunmu akwai kamar yadda na fara ambatawa karya da son birge mutane, ba ka/ki da gashin wance ki ce sai kinyi kitson wance.

Wannan ya haifar da abubuwa masu nasaba da abin kunya, domin are aren kayan bukata da kuma nuna lallai sai bikin wance ya zarta na wance, hakan ne ya jawo wasu abubuwa da suka gurbata kyawawan al’adun bahaushe;

Gurbacewar Bikin Aure A Kasar Hausa

“Abin fahari abin sha’awa al’adunmu ‘yan Kasar Hausa. Kyawun  asali da tushe a ko ina an san kasar Hausa…..” Kadan kenan daga cikin Baitocin wakar Mai Asayyaro da yake nuni da kuma tabbatar da irin tsari mai kyau na al’adun rayuwar Kasar Hausa, wanda tun asali aka san Malam Bahaushe dasu. Tabbas haka yake musamman in mukai duba da irin yadda al’ummomi cikin fadin duniya ke nuna hakilo da sha’awarsu dangane da al’adun kasar Hausa.

Biki, bidiri, burede shi ne kirarin da ake wa Bikin aure wanda ya na daya daga cikin abubuwa masu matukar mihimmanci a al’adar hausawa, akan sanya ranar bikin aure na tsawon lokaci don samun damar shiryawa tsaf don tunkarar bikin. Akan tanadi abubuwa daban daban da suka hada da kayan abinci, tufafin ado da kawa da sauran abubuwa na al’ada domin kece raini da fita kunya.

A bikin aure iyayen amarya sunfi maida da hankali kasancewar su zasu wanke su bayar, shi yasa hagulgulan bikin suka fi yawa a gidan amare, a al’adance yayin da bangaren amarya suke gudanar da kamun amarya, sa lalle, wunin biki, kafi, wankan amarya, rakiyar amarya, budar kai har zuwa ranar da baki zasu watse, su ma dangin angon a nasu bangaren ba a barsu a baya ba, domin akwai shagulgula da suka hada da kamun ango, daurin aure, zaman ajo, chuda, sayen baki da kuma tasani.

Haka kuma saboda kawaici ka mun kai da kuma kunyar malam bahaushe, dukkan wadannan sabgogin bikin na al’ada ba inda ake cudanya maza da mata sai wajen sayen baki inda abokan ango da kawayen amarya ke yin rakiya. Wadannan abubuwan su aka fi sani a kasar hausa wajen gabatar da bikin aure, koda yake a wasu lokutan al’adun sukan sha bamban daga gari zuwa gari a fadin kasar hausa, amma akasari akwai kamanceceniya a bikin kanawa, katsinawa, hadejawa, zazzagawa, sakkwatawa da dai sauran garuruwan hausawa.

Sai dai kash! Abin takaici a halin yanzu an gurbata bikin aure a kasar Hausa ta hanyar aron al’adu wadanda basu da kyau kuma basu dace da hausawa ba kwata kwata, aka gwamasu da na hausawa, a wasu lokutan ma da yawa akan watsar da zubi da tsarin bikin aure na al’ada a dauko na zamani wanda ke cike da rashin kunya da zubar da kima a tsakanin surukai, dangi da kuma ma’auratan. Abinda yasa nace haka shi ne, a halin yanzu dabi’ar turawan yamma ta mamaye bukukuwa a kasar hausa ta inda tun a farko kafin akai ga daura aure a lokuta da dama wasu angwaye da amare kan dauki hotuna na rashin kunya da takaici da sunan yin amfani dasu a abubuwan da za’a raba kyauta a wajen biki, sai kaga a tsakiyar kasuwa ana yawo da jaka ko wani abu dauke da hoton amarya da ango, ‘ya’yan hausawa cikin fita ko shiga mara mutunci da kamala, wadannan hotunan suna ciwa jama’a masu kishin addini tuwo a kwarya, don kuwa abin na neman zama al’ada. Yanzu kam hatta kamun amarya zamani ya gurbata shi, akan gudanar dashi a gwamatse maza da mata, iyaye, yan uwa, abokai da kawayen ango da amarya, ana kida ana rawa har ta kai ga uwar amarya zata iya fitowa ta taka rawa a gaban surukinta da abokansa harma su yi mata likin kudi, haka shima ango da amarya za’a basu fage don su taka rawa a gaban surukansu. Tab! Allah wadaran naka ya lalace. Abinda na sani na al’ada dangane da kamun amarya shi ne amarya kan gudu wani wurin da ba’a sani ba, akan kuma sha wahala wajen nemanta gida-gida kafin a gano inda take don a kamata, amma yanzu kam a bayyane amarya ke zuwa da kafarta wajen da aka tanada don yin kamu cikin taron maza da mata har wani lokacin ma a yanka Kek, ango ya sawa amarya a bakinta ita ta yanko ta sanya masa a baki wai duk a wajen kamu, Tirkashi! Me ne ya kawo dabi’ar Yahudu da Nasara kasar Hausa? Na san a iya cewa zuwan turawan mulkin mallaka ne ya kawo irin wannan badakalar musamman yadda suka nuna fifikon al’adunsu fiye da namu kuma wai wasunmu suka aminta da hakan madadin muyi riko da namu mu kuma nuna musu mun fisu tinkaho da alfahari da al’adunmu na kasar hausa.

Yanzu har akwai shagulgulan da akewa lakabi da (European night, Indian night Arabian night da sauransu) inda ake rakashewa da holewa dai dai da tarbiyar jinsin mutanen da aka ambata a wannan daren. Duk da yake wasu al’adun bahaushe basu dace da addini ba, amma tambaya ta anan itace shin da mu da turawan yamma su waye al’adunsu suka fi cin karo da addinin musulunci?

Akwai bukatar duba izuwa addini da al’adu masu kyau wajen tafiyar da rayuwarmu musamman wajen gudanar da bukukuwan aure don kada mu rika aiwatar da abubuwan da Allah zai fushi da shi tun a lokacin gudanar da shagulgulansa.

Ba wai cuadanya maza da mata ne a halin yanzu ke barazana da kyawawan dabi’u da al’adunmu ba, har da yadda ake almubazzaranci da dukiya, Batun anko na zaman babbar matsala cikin rukunan al’adun da muka aro, kuma yanzu ya zama tamkar gobara daga teku. A lokacin wani bikin sai ka tarar da anko kala uku zuwa hudu, kuma a wasu lokuta matsalar anko na yin sanadiyyar wargajewa wani auren.

Haka kuma batun walima mai makon tunda aure aka daura kuma zama za’a shiga wanda ake fatan mutu ka raba, sai a kwashi dukiya aje a kama wani wurin taro wanda ake kira Ebent centre a narka dukiya, akarshe idan ba’a yi sa’a bayan biki sai hangi ango ya yi tagumo. Idan kuma daman mawadaci ne ai kamata ya yi ayi amfani da wannan dukiya wajen tallafawa makwabta, wanda wani daga cikin wadanda ke yin irin wannan ragabza sai ka tarar a makwabtansa wani lokacin ko abinci iyalinsa basu ci ba.

Iyaye na da muhimmiyar gudummawa wajen gujewa irin wannan tabargazar da ake aikatawa da sunan wayewar zamani. Na tabbata irin sabgogin bikin hausawa wadanda na ambata a baya suna da matukar tasiri wajen kiyaye mutuncin ma’aurata a tsakanin dangi da abokan arziki, kuma addinin musulunci wanda hausawa suka karba ya yi hani da cudanya tsakanin maza da mata don gudun afkuwar wata badalar, saboda haka tilas ne mu guji dukkan abinda zai kawo debewar albarkar aure.

Sakamakon aro wadancan munanan al’adu yasa yanzu wata annoba mai kama da goabarar daji ta tunkaro batun aure, wannan matsala itace batun an ko wanda a wasu lokuta lamarin kan yi sanadiyyar rugujewar aure tun kafin akai ga daura shi. Misali zaka tarar da wani bikin an fitar da anko kala biyar kuma kowanne daga cikin ankon zai lashe dubban nairori, na bangaren ango daban haka ma bangaren amarya.

Ga kuma wata mummunar al’adar tafiya wuraren kwalliya irin na zamani wanda abinda ake kashewa a lokutan wannan kwalliya lamarin sai wanda ya gani. Duk da cewa kowa ya kwana da sanin irin halin da al’umma ke ciki, amma sai ko dai bangaren amarya su kekasa kasa dole sai anyi masu abu kaza da abu kaza, idan aka samu kuskuren karancin masu gidan rana shi kenan sai kaji an fara cewa mu tsoron da muke kar ka sayar da akuya ta kuma dawo tana ci maka danga.

Dubi batun gwagwaro shi kansa yanzu zaman kasa yake wata amaryar sai an nada mata kala biyar zuwa goma, domin duk kalar ankon da zata fito dashi irin kalar gwaggwaronsa daban, azo kan maganar kek, wani angon ma bai taba lasar kek ba amma ance sai  ya samar kuma tare ake so su yanka ya sawa amarya abaki itama ta sa masa ana sa bakin. Wasu manazarta na ganin mazajen da suka kashe kudi mai yawa wajen yin aure sun fi darraja matan nasu, wadanda kuma suka auro matan su cikin sauki suke wulakanta matan bayan aure. ke da araha a cikin Kasar.

Malama Zahra’u Umar mataimakiyar babban kwamanda hukumar Hisba ta Jihar Kano ta ko ka kwarai bisa yadda aka mayar da aro al’adun Nasara a matsayin ya yi, tace kulluma aikin da hukumar Hisba ke yi kenan Amru bil Ma;arufi, Wannahayu Anil’munkari, kuma kullum jan hankalin da hukumar Hisba keyi bai wuce sa tsoron Allah aduk al’amuran yau da kullum ba, domin duk lokacin da aka shigar da karya cikin harkar aure to ba shakka an dauko hanyar rusa ruhin auren.

Bai kamata ace a dinga kamfatar dukiya ana narka a wurin da Ubangiji fushi zai da duk wurin da ake aikata irin wancan badala, Idan Allah ya hore maka ba’ace karka wassa’a ba amma dai ayi bil-ma’arufi.

Aminu Muhammad direban adaidaita sahu cewa ya yi yin anko a ganinsa ai matsayi ne, saboda haka tunda lokacin ne ya zo dashi muna lale marharbin da shi.“Ni inaso na ga ana fantamawa alokacin biki, ai iya kudinka iyan shagalinka,” inji Aminu mai adaidaita sahu.

 

Exit mobile version