Bayan an kasa cimma matsaya a tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar kwadugo (NLC) na tsawan kwanaki biyu, kungiyar kwadugo tare da hadin gwiwar shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) sun gudanar da zanga-zangar adawa da cire tallafin mai a dukkan fadin kasar nan.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sabuwar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta fara dandana zafin yajin aiki, domin a makon da ya gabata kungiyar likitoci ta tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani sakamakon kin biya musu bukatocinsu, inda a yanzu kuma kungiyar NLC na gudanar da yajin aiki tare da zanga-zangar adawa da cire tallafin mai.
- Gwarzo, Bagudu Da Matawalle Na Cikin Jerin Ministocin Tinubu, Kashi Na Biyu
- An Fara Taron Harkokin Sufurin Jiragen Sama Ta 2023 A HK
Yajin aiki tare da zanga-zangar da kungiyar kwadugo ta shirya ya fara aiki ne tun a ranar Laraba domin nuna wa gwamnatin tarayya adawa da cire tallafin mai da ya haifar da tsadar rayuwa a fadin kasar nan.
Ko a ranar Talata, ma’aikatan mai sun gudanar da zanga-zanga tare da rufe ofishin hukumar kula da harkokin mai na kasa da ke Legas, yayin da kuma suka sha alwashin rufe ofisoshin hukumar a fadin kasar.
Da yake magana kan yajin aikin, Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce kungiyoyin kwadugon ba za su dakatar da zanga-zangar da yajin aikin da suka shirya yi na kasar nan ba har sai gwamnati ta biya musu bukato-cinsu.
Ajaero ya bayyana haka ne sa’o’i kadan bayan wani taron tattaunawa da kwamitin da shugaban kasa ya kafa a fadarsa da ke Abuja, ya gagara yin sulhu.
Gwamnatin tarayya dai ta yi wani yunkuri na dakile yajin aikin da zanga-zanga wanda ta gana da shugabannin kungiyoyin NLC da TUC a ranar Litinin da ta gabata, amma kuma lamarin ya ci tura.
Idan ba a manta ba dai an samu sabani tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago biyo bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu yayi a ranar 29 ga watan Mayu 2023.
A kokarin da gwamnatin ke yi na samar da sahalaha, gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai duba bukatun kungiyoyin kwadugo na neman karin albashin kashi 300 domin bai wa ma’aikata damar tun-karar kalubalen tabarbarewar tattalin arzikin da ya biyo bayan cire tallafin mai.
Duk da cewa an bai wa kwamatin tsawon makonni takwas domin ya fito da tsarin da ya dace ga ma’aikata da ‘yan Nijeriya baki daya, shugabannin kungiyar kwadugon sun dage cewa kwamitin ya ci gaba da nuna rashin jajircewa wajen cimma burinsu.
Matakin farko da shugabannin kwadugo suka yi na shiga yajin aikin ya hadu da fushin kotu wanda ta hana kungiyar.
Da yake jawabi tun da farko bayan ganawar da jami’an gwamnatin tarayya, babban sakataren kungiyar ta NLC, Emmanuel Ugboaja, ya yi nuni da cewa tattaunawar bai samu cimma matsaya ba.
Sai dai mataimakin shugaban kungiyar ta NLC, Titus Amba ya bayyana cewa babu wani sabon abu da aka samu biyo bayan jawabin Shugaban Tinubu da ya yi a yammacin ranar Litinin.
Ya ce Tinubu ya kaddamar da tallafi na naira biliyan 500 wanda za a raba wa masana’antun da kananan ‘yan kasuwa da manoma.
A yayin gudanar da wannan zanga-zangar, mambobin kungiyoyin NLC da na TUC da kungiyoyin farar hula, sun bijire wa shingen tsaro tare da karya kofar shiga majalisar wakilai domin shiga harabar majalisar, don nuna adawa da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Majalisar dattawa ta kafa wani kwamiti da zai tattauna da kungiyoyin ma’aikata da suka yi zanga-zanga bayan sun tilastawa ciki harabar majalisar dokokin kasar don nuna rashin amincewarsu da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne tun daga ‘Unity Fountain’ da ke Abuja har zuwa harabar majalisar dokokin kasar domin nuna adawa da manufofin gwamnatin Shugaba Tinubu na cire tallafin mai.
Nan take Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya shiga wata ganawar sirri da ‘yan majalisar, kuma da fitowar sa daga ganawar, ya ce majalisar dattawa ta kafa wani kwamiti mai mutane uku da zai gana da masu zanga-zangar a harabar zauren majalisar.
Kwamitin ya samu jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu da Sanata mai wakiltar Abuja, Heebah Ireti Kingibe da Sanatan Anam-bra ta Kudu, Tony Nwoye da dai sauransu.
Majalisar dattawan ta kuma kuduri aniyar cewa nan da dan kankanin lokaci za ta gana da shugabannin NLC da TUC domin ganin an shawo kan matsalar da ake fama da ita a halin yanzu.
An ga sanatocin suna tattaunawa da Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da takwaransa na kungiyar TUC, Festus Osifo.
Kungiyoyin kwadugon da suka hada da TUC da sauran kungiyoyin sun fara gudanar da zanga-zanga a Babban Birnin Tarayya Abuja, da sauran jihohin tarayyar kasar da suka hada da Legas, Abiya, Filato, Ka-duna, Kano, Ribas, Zamfara, Katsina, Kuros Ribas, Ebonyi, Inugu, Kwara, Ogun, Imo, Ondo, da Edo, da dai sauransu.
Wakilinmu Jihar Kano Abdullahi Sheka ya ruwaito mana cewa, kamar sauran takororinta na fadin kasa baki daya, an gudanar da zanga-zangar lumana wanda shugaban kungiyar NLC reshen Jihar Kano, Kwamared Kabiru Munjibir ya jagoranta, a lokacin da yake gabatar sakon kungiyar ga gwamna zuwa ga Shugaban Tinubu, na nuna adawa da cire tallafin mai.
Shi ma wakilinmu na Jihar Nasarawa, Zubairu M Lawal ya labarta mana cewa, kungiyar kwadugo ta kasa reshen Jihar Nasarawa tabi sahun takwarorinta na jihohi 36 da ke fadin tarayyar Nijariya wajen gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da cire tallafin man fetur.
Zanga-zangar da ya gudana a Lafiya fadar Gwamnatin Jihar Nasarawa ya taso ne daga Mahadar Total zuwa harabar ofishin mataimakin gwamnan Jihar Nasarawa.
Da yake jawabi Shugaban kungiyar kwadago reshen Jihar Nasarawa, Kwamared Isma’ila Ayuba Oko, ya ce kuddurin gwamnatin Tinubu ta zoma ‘yan Nijariya da cutarwa.
Zangar-zangar kungiyar kwadago a Jihar Nasarawa