A ranar Talata ne Babban Bankin Nijeriya ya sanar da sabbin dokoki na mu’amala da hulda da naira a fadin tarayyar Nijeriya.
Sabbin dokokin sun shafi ka’idar yawan kudaden da ya kamata mutum daya ko Kamfani zai iya karba a lokaci daya, dokar za ta fara aiki ne daga ranar 9 ga watan Janairu na shekarar 2023.
Sanarwar wanda Darakta mai kula da harkokin bankuna, Haruna B. Mustafa ya sanya wa hannu ta bayyana cewa, a halin yanzu an kayyade wa mutum daya karbar Naira dubu dari daga banki ko kuma kowacce kafa ta karbar kudi kamar POS da ATM a mako daya yayin Kamfanoni kuma aka kayyade musu karbar Naira 500,000 a mako daya. Ga dai abubuwa 6 da ya kamata al’umma su lura dasu kamar haka.
1. Yawan kudin da mutum daya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.
Idan mutum na son cire kudin da ya fi wannan adadi yawa to sai an caje shi kashi 5 cikin 100 ga mutum da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da zai cire.
2. Duk wanda ya je banki cire kudin da suka haura naira 50,000 da caki na banki da wani ya rubuta masa, to ba za a ba shi kudin ba. Yayin da dokar cire kudin da suka kai naira miliyan 10 ta amfani da caki a tsakanin bankuna daban-daban tana nan a yadda yake.
3. Yawan kudin da mutum zai iya cirewa ta hanyar amfani da na’urar cire kudi ta ATM a sati kuwa shi ne naira 100,000, wato yawan abin da za a cire a rana shi ne naira 20,000 ne kacal.
4. Takardun kudin naira 200 kawai bankuna za su dinga lodawa a cikin na’urar ATM.
5. Idan a wajen masu amfani da na’urar POS ne kuwa, naira 20,000 ce yawan kudin da mutum zai iya cirewa.
6. A yanayin da ake da tsananin bukata kuwa da ba zai wuce sau daya a wata ba, inda ake bukatar cire kudin da yawansu ya fi wanda aka kayyade don wani dalili mai karfi, to abin da za a bari mutum ya cire ba zai haura naira miliyan biyar ba, idan kuma kamfani ne to ba zai haura naira miliyan 10 ba.
Sannan a hakan ma sai an caji kashi biyar cikin 100 na yawan kudin ga mutum, da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da za a cire.
A tsokacinsa a kan sabbin dokokin, wani masani a bangaren tattalin arziki, Kwamrade Shafii Ibrahim Idris, ya ce, “Dokar na da fuskoki biyu, fuska ta farko, wannan dokar za ta shafi kananan ‘yan kasuwa masu ciniki sannan za ta shafi har manyan masu kasuwnci wadanda basa amfani da asusun ajiya a banki domin daga wannan lokaci kudaden naira za su yi wahalar yawo sosai. Hakan kuwa zai shafi duk mai kasuwancin da yake mu’amula da kudi a hannu kawai”.
Ya kuma bayar da shawara ga ‘yan kasuwa da su gaggauta bude bude asusun banki domin tserar da cinikinsu, ‘Bawai don wannan tsarin ba kawai, bude asusun banki yana da alfanu masu yawa’ in ji shi.
“A daya fuskar kuma, karancin da kudaden naira za su yi zai daga darajarta wanda a sanadin hakan za ta kara farfadowa wanda muna fatan za ta zama sa’ar dalar Amurka”, in ji shi.