ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

by Sani Anwar and Sulaiman
1 year ago
jam'iyyu

“Matsala na nan tafe, amma hakan ba yana nufin a sama mata wajen zama ba.” Karin maganar Afirka.

Babban abin takaici shi ne, yadda ake tilasta wa al’ummar kasar nan kallon zazzafar rigimar da ke tunkaro zaben 2027, yayin da rage kasa da shekaru biyu a gudanar da shi.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Dukufa Wajen Karya Farashin Kayan Abinci – Minista
  • Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6

Kalli dai yadda gwamnatin Tinubu ke faman kokarin fito da tallafin da bai taka kara ya karya ba da wasu alkawarurruka a matsayin nasarar da ta samu cikin shekaru biyu. Yayin da babbar jam’iyyar adawa kuma ke ikrarin cewa, gwamnatin ta dauki hanyar rugujewa.

ADVERTISEMENT

Wasu daga cikin ‘yan siyasa na kokarin hada kai, amma girman kai da bukata ta kashin kai, ta hana su aiwatar da hakan. Haka zalika, al’umma na kallon tsananin tashin hankali da damuwa kan makomarta, inda su kuma ‘yan siyasa ke ci gaba da bayyana karyar cewa, ana aiwatar da demokuradiyyar Nijeriya ne; domin al’umma.

Yayin da ya rage saura shekaru biyu, abin da aka tsara shi ne; yin nasara a kan ‘yan adawa, tun kafin lokacin zaben ya gabato. Jam’iyyar APC ta sauya akalar siyasa ta hanyar amfani da wasu dabaru tare da dakile dukkanin wasu damammaki. Don haka, kowa zai yi burin shigowa, hatta wadanda suka suka bar jam’iyyunsu na PDP da LP, ba su da wani wurin zuwa a daidai wannan lokaci.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Babu abin da ya rage yanzu, illa babatun zantukan siyasa da ‘yan siyasar ke ta fama yi a kasar, wadanda suka jarabtu da matukar son mulki. Wannan abu da ke faruwa yanzu, ko shakka babu zai canja, zai canja din ne kuwa yayin da ‘yan siyasar ke aiwatar da tsare-tsarensu, sai masu jefa kuri’u a Nijeriya kuma su yanke hukunci. Shekarar 2027, za ta kasance mai ban mamaki tare da kalubale ga ‘yan Nijeriya.

A bisa dukkan alamu, jam’iyyar APC ta dukufa wajen kara habaka karfinta ne kawai da ganimar ‘yan adawa. Tana ta faman sa kanta cikin rigingimu, har wadanda ba su shafe ta ba a cikin shekaru biyun da ya rage mata ta yi gaba na kunci da tsanani. Maimakon gwamnatin ta mayar da hankali kan nauye-nauyen da ke kanta, na yi wa al’ummar kasa aiki; sai ta buge da yin fada da jam’iyyar adawa, kullum cikin wasa wukarta; a gefe guda kuma gazawar gwamnatin na fitowa fili.

Kura-kuren gwamnatin sun hada da; girman kai wajen tafiyar da al’amuranta, rashin tafiyar da abubuwa yadda ya kamata; tunanin cewa, jawo ‘yan adawa zai ba ta dama tare da karfin yin fada da kuma lashe zabe; ta hanyar zaben shugaban kasa cikin sauki, wanda kowane bangare zai bayar da gudunmawarsa. Amma, babbar matsalar ita ce; shugaban kasar ba shi da kima a kusan dukkanin sassan kasar.

Jam’iyya mai mulki, za ta iya bunkasa damar da take da ita, idan ba ta tsayar da Tinubu a 2027 ba, musamman idan za ta tsayar da matashi, lafiyayye, dan siyasa mai gaskiya da son ci gaba. Hakan kuwa, da alamu ba zai yiwu ba, domin Tinubu shi ne ked a wuka da nama a jam’iyyar.

Shugaban kasa da kansa, ba zai iya bayar da shawarar yadda za a yi gyara ta hanyar kawo wani dan takarar da ya dace ba. Idan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, zai kasance a matsayin dan takara, APC za ta yi amfani da dukkanin damammakin da take das u, musamman na amfani da kudi wajen sayen kuri’u da masu zabe. Rage Muslman Arewa saboda Kiristocin Arewa, na iya zama hadari, amma wannan shi ne kawai abin da za a iya yi.

Haka zalika, jam’iyyar ta zama dakikiyar daliba, domin babu abin da take karantawa illa yadda za ta samu damammaki iri daban-daban na siyasa kadai. Dandazon da ‘yan siyasa suka yi a cikinta, ba karamar barazana ba ce ga masu bukatu daban-daban, musamman idan aka kasa biya musu bukatunsu.

Ko shakka babu, Arewa za ta yi matukar tasiri a zaben da za a yi. Shi ne yankin day a fuskantar ayyukan ta’addanci da kuma mummunan talauci da ke biye da su har zuwa rumfunansu na zabe. Saboda haka, dole ne jam’iyyar ta yi aiki tukur don kaucewa sake faruwar zaben 2015, lokacin da jam’iyya mai mulki ta fuskanci daukacin yankin da suka yi mata zanga-zanga.

Kudu-maso-yamma, za su iya goyon bayansa idan ya kasance manyan ‘yan adawa sun fitar da wani dan takarar daga Arewa, amma wannan rashin kwanciyar hankali da ake fama das hi, ya kamata a ce ya hana kowa barci.

Tasirin Wike, zai iya raunanawa ko karfafawa; ya danganta da matakin da ‘yan adawa suka dauka game da rikice-rikice a Kudu-maso-kudu, wanda zai iya daidai da bukatunsu; ba abubuwan da suka dace ba. Za a lalata jam’iyyar LP ba tare da Obi ba, a kuma matse shi a matsayinsa na dan takararta.

Burin Obi yanzu, ya wuce batun jam’iyyar LP; amma akwai barazanar samun raguwa a matsayinsa na dan siyasa, idan ya yanke shawarar da za ta iya raba mabiyansa. Kudu-maso-gabas, sun kagu su ga sun samu mukamin shugabancin kasa, wanda hakan ke nuna kishinta na samun daidaito. Hakan, na iya yiwuwa ta hanyar samun daidaito, ana iya samun hakan ta hanyar yarjejeniya a tsakanin yankunan da ake da su.

Da alamu dai, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne ke da babbar matsala. Ya yi rauni da yawa da zai iya ja da bukatar Tinubu na neman wa’adi na biyu. Don haka, sake barin jam’iyyar PDP tare da neman wata jam’iyyar daban, hanya ce kawai ta kasha makudan kudade da bata lokaci da sauran makamantansu.

PDP a halin yanzu, na zub da jini ne sakamakon zagon kasan da jam’iyya mai mulki ke yi mata. Babbar kadararta shi ne Atiku, amma kuma shi ne babbar matsalarta. Matsayinsa na farko a jam’iyyar, shi ne ke haifar da korafe-korafe da rudani, zai yi wuya PDP tare da Atiku su shiga yarjejeniyar da za ta bayar da dama a karo na biyu.

Idan da PDP za ta iya gyaruwa ta samu nasara a kan APC, dab a ta damu da neman biyan bukatun da suka fi muni ko kawo rudani ba. Jam’iyyar da ta taba yi wa al’ummar kasar barazana, yanzu kuma tana cikin sadar kafa tarihi wajen rubuta ta a matsayin wacce da fi bayar da gudunmawa wajen samun nasarar APC 2027.

Zaben 2027
Sani Anwar
+ posts Bio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta
Zaben 2027
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Taron Koli Na Sin Da Kasashen Yankin Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu Zai Ingiza Manufar Kara Dunkulewar Sassan Yankin

Taron Koli Na Sin Da Kasashen Yankin Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu Zai Ingiza Manufar Kara Dunkulewar Sassan Yankin

LABARAI MASU NASABA

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.