Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron manema labarai na yau cewa, bayan gwamnatin kasar Sin ta fitar da shirinta na kyautata kandagarkin cutar COVID-19 da mayar da cutar zuwa rukunin B daga rukunin A da kuma kyautata matakan tafiye- tafiye tsakanin Sin da kasashen waje, yaduwar annobar ta ragu sosai a kasar, kuma adadin mutanen dake shiga kasar da ma fita, ya karu.
Wang Wenbin ya kara da cewa, harkokin samar da kayayyaki da na rayuwar yau da kullum sun dawo kamar yadda suke a baya, kana sha’awar Sinawa ta zuwa ketare ta karu sosai, haka kuma an kyautata sharuddan dawo da harkokin yawon bude ido. (Fa’iza)