Adadin wadanda suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kai wa tun da aka fara yaki tsakanin dakarun kasar da mayakan Hamas ya zarce 38,000, a daidai lokacin da rikicin ke shiga wata na 10.
Ma’aikatar lafiyar Gaza, wadda ke karkashin ikon Hamas ce, cikin wata sanarwa ta bayyana adadin wadanda suka mutu tun da yakin ya barke a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
- Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Masu Bayyana Ra’ayoyi Suka Zargi Nuna Fin Karfi Da Amurka Ta Yi A Harkokin Intanet
- AI Da Sabon Karfin Samar Da Hajoji Da Hidimomi Masu Karko
Kazalika, sanarwar ta kara da cewa jimillar wadanda suka jikkata ya zuwa yanzu ya kai 87,828, biyo bayan hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin Zirin Gaza.
Sanarwar ta ci gaba da cewa a cikin sa’o’i 25 da suka wuce, Falasdinawa 55 ne suka yi shahada, kana 123 suka samu raunuka a hare-haren baya-bayan nan da dakarun Isra’ila ke kai wa Gaza a kokarin da suke ci ga da yi na kakkabe mayakan Hamas.
Wannan na zuwa ne a dadai lokacin da Hamas ta ce tana jiran martani daga Isra’ila a game da tayin tsagaita wuta da ta mika, kamar yadda wasu jami’anta biyu, wadanda suka nemi a sakaya sunayensu suka bayyana a wannan Lahadi, kwanaki 5 bayan da ta amince da wani muhimmin sashe a cikin shirin Amurka na kawo karshen wannan rikici da ya shiga wata na 10.