ADC Ta Gudanar Da Zaben Sabbin Shugabanninta A Adamawa

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ta gudanar da zaben shugabannin da zasu jagoranci jam’iyyar na tsawon shekaru hudu a jihar Adamawa.

Zaben wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana, an zabe Yahya Hammanjolde, a matsayin shugaban jam’iyyar da kuri’u 417 da Musa Hamman Adama matsayin sakataren jam’iyyar da kuma Aisha Bello, shugabar mata da dai sauransu.

Da take rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar jami’a mai baiwa jam’iyyar shawara ta fuskacin shari’a Baresta Justine Abanida, ta shawarci sabbin shugabannin jam’iyyar da suyi komai na jam’iyyar bisa gaskiya da adalci kamar yadda suka rantse akai.

Tun da farko jami’in sa’ido game da zaben da uwar jam’iyyar ta nada Ibrahim Manzo, ya bayyana yadda zaben ya gudana da cewa na nuni da jam’iyyar ADC ta kafu daram a jihar Adamawa.

Saboda haka ya bukaci jama’ar jihar da su amshi jami’iyyar domin acewarsa itace wacce zata share musu hawaye a babban zaben dake tafe a jihar da kasa baki daya.

Shima da yake jawabi mamba a kwamitin gudanar da zaben Umaru Kugama, ya ce basu dauki batun kafa jam’iyyar ADC a jihar da wasa ba, “ba batu ne na wasa ba, munzo neman mu kafa gwamnati ne kuma zamu samu”.

Haka shima sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa wanda ya canja sheka zuwa jam’iyyar ADC Sanata Abdul’aziz Nyako, ya ce wannan ranar ranace ta farin ciki a gareshi domin kuwa mafarkinsa ya zama gaskiya.

Ya ce zai tabbatar sunyi duk abinda zasu iya na ganin sun kwace gwamnati a hanun jam’iyyar APC a jihar a babban zaben 2019.

Ya ce sunyi iya bakin iyawarsu jam’iyyar APC tayi a zaben shugabannin jam’iyyar da ya gudana, amma hakarsu bata cimma ruwa ba, don haka suka kawo jam’iyyar ADC domin sharewa jama’ar jihar hawaye a zabe mai zuwa.

Shima dai sabon shugaban jam’iyyar ADC a jihar Yahya Hammanjolde, ya gode da zabensa da aka yi, ya kuma yi alkawarin yin aiki da gaskiya domin kai jam’iyyar ga nasara.

 

 

 

Exit mobile version