Jam’iyyar hadaka ta ADC ta umurci dukkan ‘ya’yanta ta su yi murabus daga jam’iyyunsu na asali, sai dai ba ta fayyace lokacin da za a fara bin wannan umarnin ba.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan ga ‘yan jarida a Abuja ranar Alhamis bayan wani taro na musamman da manyan shugabannin jam’iyya da ‘yan siyasa suka halarta.
- Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
- Dubban Matasan Kano Sun Yi Zanga-zangar Lumana Domin Goyon Bayan CP AI Bakori
“Ko da yake an ba da umarnin karshe ga duk mambobi su yi murabus daga sauran jam’iyyun siyasa, amma jam’iyyar ba ta yi magana kan lokacin karshe da ta ajiye ba na fara bin umurnin,” in ji Abdullahi.
Haka kuma jam’iyyar ta sanar da duk batutuwan da suka shafeta da jam’iyyar ADA, wanda ta ce an riga an kammala komi a matsakani.
A cewar Abdullahi, “Hadakar jam’iyyar ADC fayyace komai dangane da batutuwan da suka shafi kawancen siyasa da ADA. Wannan na nufin, ba su da sha’awar rajista da kungiyar ko akasin haka.”
A kan zaben 2027, Abdullahi ya ce ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar sun yarda za su goyi bayan duk wanda ya lashe zaben fid da gwani.
“Dukkan ‘yan takarar shugaban kasarmu sun yarda za su goyi bayan wanda ya ci zaben fid da gwani da jam’iyyar za ta gudanar,” in ji shi.
Ya kara bayyana cewa nan gaba kadan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar zai sanar da ranakun zaben fid da gwani a Osun da Ekiti kafin zaben gwamna a kowace jiha.
Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Dabid Mark da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da sakataren jam’iyyar na kasa, Ogbeni Rauf da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai da tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Tambuwal da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Chibuike Amaechi.
Sai dai kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, bai halarci taron ba, amma ya aika da sako tare da tabbatar da jajircewarsa ga hadakar jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp