Umar A Hunkuyi" />

Addu’a Da Gyaran Halayenmu Ne Mafita Kan Matsalar Tsaron Kasar Nan – Alhaji Tahir

A kullum muna yi wa Allah godiya da bai duba halayenmu ba, ya ba mu yanayi mai kyau mai albarka a wannan kasar tamu.

Wadannan kalaman sun fito ne daga bakin Alhaji Awwal Tahir, wani dan kasuwa kuma manomi a garin Kaduna, a lokacin da yake Magana a kan matsalolin tsaron da suka addabi al’ummar kasar nan.

Awwal Tahir ya ci gaba da cewa; “Hakika Allah Ya saukar mana da ruwa, kuma gwamnati ta bai wa  wasu taki, duk da cewa ba ma takin ne matsala ba a halin yanzun a wannan kasar tamu. Matsalar mu ita ce batun tsaro, misali kamar ni ina da gona a Maru, ta nan in ka wuce Sarkin Pawa, gonar tawa ta fi girma da fadin hekta 100, amma rabon da na ko leka gonar nan tawa yanzun ya fi shekara uku, domin kamar yanda aka ma shaida mani shi ne, masu satar mutane a gonar tawa ne suka yi sansaninsu, ashe ka ga ba hauka nake ba na je na kai kaina. Wannan matsalar tsaron kuma shi zai hana samun amfanin gona yanda ya kamata. Batun noma za a yi noma, amma sai dan na wadanda za su noma abin da za su dan ci a bayan gidansu haka, amma wannan ba shi ne zai ciyar da kasa ba. wanda zai noma buhuna dubu uku, dubu hudu, biyar zuwa ma sama wannan shi ne zai ciyar da kasa, wanda a halin yanzun ya gagara saboda matsalar tsaro a wannan kasar.

Ni a nawa ganin matsalar tsaron nan halinmu ne, don haka wajibi ne mu ji tsoron Allah mu koma wa Allah. Duk da hanyar rokon Allah da nake nufi a nan ta yi kama da abin da wasu za su ga tsohon yayi ne, amma lallai mu koma ga Allah, mu roki Allah gafara a bisa abin da muke aikatawa marasa kyau.

A lokacin muna yara, Sarakuna, dagatai, Hakimai da masu unugwanni a kowace ranar Juma’a sukan tara malamai da sauran al’umma da misalin karfe 10 zuwa 11 na safiya a yi rokon Allah domin neman yalwa da kariya a bisa masifu, sannan kuma a yi Sallar Juma’a nan ma a gayawa Allah, mu kuma gyara halayenmu. To sai ka ga Allah ya yi mana ludufi da abu ma kyau, Ya kange mu daga munana.

Kamar yanda na fada, tilas  ne mu gode wa Allah, domin da Allah Ya duba halayenmu da mun fi haka kokawa. Ko maganar koronan nan, a gaskiya akwai ta, amma sam mu ba mu da tasirin koronan a nan, ka ga wannan Allah ne ya kare mana ganin tasirin koronan a nan. domin in ka dubi yanda take ta kashe mutane a wasu kasashen kamar ruwa, to wajibi ne mu a nan mu kara gode wa Allah a bisa kariyar da ya ba mu. Da matsalar tsaro da annobar koronan nan duk halayenmu ne suka janyo mana, don haka tilas sai mun nemi gafarar Allah a aikace, mun kuma roke shi kafin mu sami saukin wadannan.

Exit mobile version