Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shirya tarbar tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Super Eagles a Fadarsa da ke Villa Abuja, a yau Talata.
Ana kyautata zaton cewa, Shugaban zai yi musu godiya ne kan bajintar da suka nuna wajen kaiwa wasan karshe na kofin kasashen Afirka (AFCON 2023) da aka kammala a kasar Cote de’Voire.
- AFCON 2023: Muna Alfahari Da Yadda ‘Yan Wasan Super Eagles Suka Wakilci Nijeriya – Tinubu
- AFCON 2023: Hukumar NOA Ta Tsunduma Gangamin Tara Wa Super Eagles Ɗimbin Magoya Baya – Minista
Idan ba a manta ba LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa yan wasan da sauran jagororin tawagar ta Super Eagles akan rawar da suka taka a gasar.
Tinubu ya bayyana tawagar a matsayin jajirtattun yan kasa da suka yi iyakar kokarinsu wajen daukaka sunan kasar a idon Duniya a fagen kwallon kafa, ya kuma bukaci dukkan yan kasa da su yi kokarin kare martaba da sunan Nijeriya a duk inda suka samu kansu.