Wani matashi dan asalin garin Kagoro a karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna da ke aikin hidimar kasa (NYSC) a jihar Adamwa, ya rasa ransa lokacin da yake kallon wasan Super Eagles da Bafana Bafana na kasar Afrika ta Kudu.
Ko’odinetan hukumar matasa ‘yan yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) reshen jihar Adamawa, Mista Denis Jingi, ya tabbatar da haka ga manema labarai a Yola, ya ce tuni aka ajiye gawar Peter Yunana, a asibitin koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola.
- Za Mu Tabbatar Kotu Ta Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari – Fintiri
- Za Mu Tabbatar Kotu Ta Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari -Fintiri
Ya ce marigayi Peter mai lambar yi wa kasa hidima NYSC AD/23C/0365 da ke aikin a GSS Numan ya fadi ya mutu a daidai lokacin bugun daga kai sai mai tsaron gida, tsakanin Super Eagles da Bafana Bafana, da mariyin ya shaidawa abokan aikinsa ba zai iya ganin bugun ba.
Ya kara da cewa “Peter da sauran abokan kallonsa suna kallon wasan lokacin da aka kai bugun daga kai sai mai tsaron gida, sai ya shaida musu cewa ba zai iya kallon bugun ba, sai ya sunkuyar da kansa kasa, daga baya kuma kawai sai ya fadi.
“Abokan aikinsa sun garzaya da shi babban asibitin Numan, Amma sai aka tabbatar da cewa ya mutu, an ajiye gawarsa a cikin asibitin.
“Yanzu mun kai gawar zuwa asibitin koyarwa na FMC Yola, domin ajiye gawar zuwa lokacin da iyayensa za su shirya jana’idarsa a jihar Kaduna” inji Jingi.