Idan a dab da kai akwai wani, wanda yake da sanin kamata, da kwarewar aiki, da son cika alkawari, kana yayin da yake hulda da sauran mutane, yana da natsuwa, da kulawa da moriyar su, toh ganin kana da irin wannan mutumin kirki da za a iya dogaro da shi, ba zai sa ka yi sha’awar kulla abokantaka da shi ba?
Hakika, kasar Sin abokiyar kasashen Afirka ce, wadda halayyarta ta yi kama da ta wannan mutumin da na ba da misali.
- Eric Chelle Ya Sake Bai Wa Ahmed Musa Damar Taka Leda A Super Eagles
- Azumin Ramadan: Gwamna Buni Ya Amince Da Naira Miliyan 297 Don Ciyar Da Mutane 51,000 A Kullum
A wajen taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, da aka kaddamar da shi yau a birnin Beijing na kasar, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnati, wanda ya shaida mana yanayin tabbas da Sin take da shi daga bangarori 2:
Na farko, yadda ake samun tabbaci kan ci gaban tattalin arzkin Sin.
Idan an lura da yanayin tattalin arzikin kasar Sin, to, za a san cewa har kullum gwamnatin kasar ta kan cika alkawuran da ta yi a fannin raya tattalin arziki. Kamar yadda alkaluma daga cikin rahoton aikin gwamnatin Sin suka nuna: An yi hasashen samun karuwar GDPn kasar da ta kai kimanin kaso 5% a shekarar 2024, daga baya matsayin karuwar da ta cimma shi ne kaso 5%. Kana an yi hasashen samun sabbin guraben aikin yi fiye da miliyan 12 a birane da garuruwan kasar, a shekarar 2024, yayin da jimilla ta hakika ita ce miliyan 12.56. Haka zalika, an yi hasashen girbin hatsi fiye da kilo biliyan 650 a kasar a bara, yayin da yawan hatsin da aka samu a karshe ya kai fiye da kilo biliyan 700. Kana kasar ta kiyaye wani yanayi na samun ci gaba mai armashi a dukkan bangarorin da suka hada da ciniki, da masana’antu, da kare muhalli, da dai sauransu. To, wannan yanayin da kasar ke ciki na samun tabbaci kan ci gaban tattalin arzikinta ya ba ta damar cika duk wani burin da ta sanya a gaba.
Na biyu, shi ne dorewar manufofin kasar Sin.
Za a iya ganin dorewar manofofin Sin, bisa tantance rahotannin aikin gwamnatinta na shekaru daban daban. Misali, a cikin rahoto na wannan karo, an ambaci manufofin raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, da habaka cudanyar kasa da kasa a fannin al’adu, da tsayawa kan niyyar amfanawa juna yayin da ake hadin gwiwa da sauran kasashe, da dai sauransu. Sai dai dukkansu tsoffin manufofin kasar Sin ne da ake ci gaba da kokarin aiwatar da su. Hakan ya nuna cewa, manufofin Sin a fannin diplamasiyya, musamman ma ta fuskar hulda da kasashen Afirka, su ma suna cikin wani yanayi na tabbas. Kamar yadda ministan wajen kasar Sin ya kan ziyarci kasashen Afirka a farkon duk wata sabuwar shekara, cikin wasu shekaru 35 a jere, ya nuna cewa kulla abokantaka da kasashen Afirka wata manufa ce ta tushe da kasar Sin take kokarin tsayawa a kanta.
To, wadannan fannoni 2 da na ambata sun tabbatar da sakamakon hadin gwiwar Sin da Afirka mai armashi.
Misali, kasar Sin ta dade da kasancewa kasar da ta fi yawan ciniki da kasashen Afirka, kana jimillar cinikinsu na ta samun karuwa. A shekarar 2024, darajar kayayyakin da aka yi cinikinsu tsakanin Sin da Afirka ta kai kimanin dalar Amurka biliyan 289.1, adadin da ya karu da kaso 6.1% bisa na shekarar 2023. Kana a bangaren zuba jari, yawan kudin da kamfanonin Sin suka zubawa kasuwannin Afirka ya kai fiye da dala biliyan 40 a karshen shekarar 2023. Yayin da a Najeriya, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar tun shekarar 2013 ta riga ta haifar da ayyukan raya kasa fiye da 3000, inda ko a cikin watanni 2 da suka gabata ma, an ga yadda wani kamfanin Sin ya kammala aikin gyara da habaka manyan titunan da suka hada Keffi da Makurdi, kana bangarorin Sin da Najeriya sun kulla yarjejeniyar kafa babbar masana’antar samar da iskar Hydrogen ta zafin hasken rana a jihar Akwa Ibom.
Hakika idan mun duba muhallin duniya, za mu ga yadda ya cika da yanayin rashin tabbas. Wanda ya samo asali daga yake-yake, da bala’u daga Indallahi, gami da canzawar ra’ayi da wasu kasashen su kan yi, misali, a jiya sun ba ka tallafi, sa’an nan yau suka dakatar da shi, toh watakila gobe ma za su bukaci ka mayar musu kudinsu. To, yayin da ake fuskantar wannan muhalli, abu ne mai kyau a samu wani aboki da za a iya dogaro da shi. Abun haka yake ko? (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp