Jiya Lahadi 1 ga watan Janairu ne, Afirka ta Kudu ta yi bikin cika shekaru 25 da kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin.
Sashen hulda da kasa da kasa na kasar, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na intanet cewa, a cikin shekaru 25 da suka gabata, kasashen biyu sun zurfafa huldar dake tsakanin su a fannoni da dama, kuma tun daga lokacin aka daukaka alakar zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da sabbin tsare-tsare na hadin gwiwa na tsawon shekaru 10, daga shekarar 2020 zuwa 2029.
A ranar 1 ga watan janairun shekarar 1998 ne, Afirka ta Kudu ta kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin. (Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp