CRI Hausa" />

Aikin Da Na’urar Tianwen-1 Ya Yi A Mars Ya Kafa Wani Sabon Tarihin Binciken Samaniya

Hukumar dake lura da ayyukan binciken sarararin samaniya ta kasar Sin CNSA, ta ce aikin binciken duniyar Mars da kasar Sin ta gudanar da kumbon Tianwen-1, ya cimma manyan nasarori guda 6, a tarihin ayyukan sama jannatin kasar, ciki har da samar da bayanan kai tsaye na kimiyya, irin su na farko ga kasar Sin daga Jar Duniya.

Tianwen-1 ya kuma zamo aikin binciken kimiyya na farko da Sin ta gudanar, wanda ya kunshi duniyoyin biyu, wato duniyar bil adama da kuma Mars, inda aka wanzar da sadarwa tsakanin nisan da ya kai kilomita miliyan 400.
Da yake tsokaci game da hakan, kakakin hukumar CNSA Xu Hongliang, ya ce wannan aiki baya ga kasancewarsa na farko da ya baiwa Sin damar ajiye alamar ta a duniyar Mars, a daya bangaren kuma, ya bada damar kewaya falakin duniyar Mars, tare da saukar na’urar bincike kan doron duniyar ta Mars a lokaci guda. Ya ce an kuma gudanar da hadin gwiwa mai gamsarwa tsakanin sassan kasa da kasa, yayin wannan aiki na Tianwen-1.
Jami’in ya ce a karo na gaba, yayin da Sin ke gudanar da ayyukan binciken duniyar wata da makamantan su, da ma shirinta na kafa cibiyar binciken sararin samaniya mallakin ta, Sin za ta yi cudanya da hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, domin wanzar da tattaunawa, da ba da gudummawa domin cin gajiya tare. (Saminu Alhassan)

Exit mobile version