Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta fara gudanar da aikin hajjin shekarar 2025 a hukumance inda tawagarta ta musamman ta tashi zuwa kasar Saudiyya. Tawagar wacce ta kunshi manyan jami’an gudanarwa da kuma manyan jami’an kungiyar likitocinta ta kasa, sun bar Abuja ne a ranar Litinin bayan wani bikin bankwana da aka gudanar a ‘Hajji House’.
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da Shafii Sani Mohammed ya rubuto daga sashin yada labarai na NAHCON.
- Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Wutar Lantarki Da Za Ta Raba Wa Jihohi 3 Wuta
- An Tsinci Gawarwakin Yara Biyar Cikin Tsohuwar Mota A Nasarawa
Da yake gabatar da Tawagar ga Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, Daraktan Gudanarwa, Alhaji Babagana Bukar, ya yabawa yadda tawagar ta nuna kwazo a aikin Hajjin da ya gabata. Don haka, ya kara amincewa da kwarewarsu. Ya kuma yi kira ga Shugaban Tawagar Gudanarwar da su ci gaba da bayar da cikakken goyon bayansu ga hukumar don ganin an sake samun nasara a wannan karon.
A nasa jawabin, shugaban NAHCON ya bukaci tawagar da ta tunkari wannan aiki tare da himma da kwazo, tare da jaddada tsarkin aikin da ke gabansu.
Wannan Tawagar ta musamman, ita ce ke da alhakin kafa harsashin gudanar da aikin Hajji baki daya, da suka hada da tsare-tsare na masaukai, ka’idojin karbar baki a filin jirgin sama na kasar Saudiyya, da hada kai da hukumomin Hajji na Saudiyya. Yunkurin nasu ya share fagen isowa da jin dadin alhazan Nijeriya, da ma’aikatan lafiya, da jami’a na jihohi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp