Connect with us

TATTAUNAWA

Aikin Jarida A Shirin Arewa 24 Ya Sa Min Kaunar Aikin Jarida A Zahiri  –Jarumi Aliyu Hussaini

Published

on

sahabi

Tattaunawar  WAKILINMU, MUSA ISHAK MUHAMMAD Tare Da JARUMI ALIYU HUSSAINI Wato SAHABI A Shirin Kwana Casa’in Na Arewa 24.

 

Da Farko Za Mu So Mu Ji Sunanka Da Kuma Takaitaccen Tarihinka. Sunana Aliyu Hussaini Musa. An haife ni ne a cikin karamar hukumar Ungogo, amma na taso ne a Indabawa da ke nan cikin garin Kano. Na yi karatuna na  Firamare  a  nan  da kuma  na sakandire. Daga nan na samu (admission) a CAS Kano, wanda ban ma kai ga kammalawa ba kuma sai na samu (admission) a nan Jami’ar Northwest, wadda yanzu  a  ka  fi  sani  da  Jami’ar Yusuf  Maitama Sule. Ina karanta Turanci ne wato (English) kuma ajina uku yanzu wato (level 3). Wannan shi ne tarihina a takaice.

Kafin  Mu  Fara  Magana A  Kan  Shirinka  Na Kwana Casa’in Wanda Da Shi Ne Ka Fi Shahara, Shin Ka Taba Fitowa A Cikin Wasu Finaf inai Ne A Baya? Eh kafin na fara Kwana Casa’in gaskiya  na  fito  a  wasu  fina-finai kamar guda shida zuwa bakwai. Kamar yadda su ma lokacin da Arewa su ka yi min tantancewa na ba su irin wannan amsar da na baka a yanzu. To na yi f ina-finai  amma  da  ya  ke  su gaskiya  ba  fitattu  bane  ba  kamar wannan. Fim dina na farko a shigowata wannan  masana’anta shi  ne  fim  din  “Farar  Zuciya”  na Kamfanin Ali Rabiu Ali (Daddy) wato A.R.A Mobies, wanda shi bai  fita  ba  ma  har  yanzu.  Bayan shi  kuma  akwai  fina-finai  irin su  Sakayya,  irinsu  Ta  Ki  Zaman Aure,  sannan  ina  cikin  fim din Mariya nasu Ali Nuhu da dai  sauransu.  Ba  zan  iya  kawo su a jere ba gaskiya yanzu. Wadannan su ne dai kadan daga cikin wadanda na yi sauran na manta su gaskiya.

Kamar Yadda Ka Fito A Matsayin  Dan  Jarida  A  Cikin Shirin Kwana Casa’in, Ko Ka  San  A  Wannan  Matsayin Zaka Fito Tun Da Farko? Eh to abinda ya ke faruwa shi ne, bari in fara baka abun tun daga mafari, ni ma kawai labari na  ji cewa  Tashar  Arewa  24  za  su yi tantancewa abinda a ke cewa (audition) na gwaji, wanda daga nan ne idan ka chanchanta sai a dauke ka. To shi ne sai na ji labarin,  amma  a  lokacin  ban  ma san  wanne  fim  za  su  yi  ba.  Shi ne  sai  na  tura  takarduna,  kuma sai a ka kirawo mu tantancewa. To bayan mun je ne sai a ka bani (script) na karanta, to a lokacin muna da yawa wadanda a ka bamu mu karanta a kan rawar da Sahabi zai taka a cikin shirin. To a wannan karatun ne na gane cewa shi Sahabi zai taka rawar Dan jarida ne a ciki. Kuma a  rayuwata  ban  taba  yin  aikin jarida ba, hasali ma kasan kowa na da irin burin da ya ke so ya ga ya zama a rayuwa to ni gaskiya kafn wannan lokacin ban taba burin in ga na zama dan jarida ba.  To  na  zo  tantancewar  ban ma san zan ci ba, sai na ke cewa kaina a matsayina na jarumi, jarumi  ko me a ka ce masa zai f ito,  to    kawai  zai  karba  ne  ya hau, sannan ya yi kokarin ganin ya bada abinda a ke da bukata. To a haka dai na yi addu’a a kan Allah ya bamu sa’a. Daga nan a ka kirawo mu a ka tantance mu, a ka ce za a neme mu. Shi ne daga baya a ka kirawo ni a kan cewa ni ne na samu nasarar wannan fitowa ta Sahabi.

To Ka Samu Wani Horo Na Musamman Ne Kafun A Fara Shirin Ko Kuma Kawai Gogewa Ka Nuna Ta Cewa Kai Kwararren Jarumi Ne? Eh to abinda ya faru gaskiya wasu matakai ne wadanda na bi. To abu na farko wanda kuma shi  ne ginshiki, shi  ne wato  shi Kamfanin  da  na  fito  na  Ali Rabiu Ali, idan ka shiga kafun a fara saka  maka  (Camera)  ka  fito  a cikin  fim  sai  ka  fara  kwarewa  kan irin dirama din nan da a ke yi ta dabe. To don haka ni na samu wannan horon kuma ina cikin irin  wadanda  za a  ce an yaye su. Sannan tunda na ga an ba ni  fitowar  Sahabi,  kuma  Sahabi zai  fito  ne  a  Dan  Jarida  nasan fa to dole sai na jajirce tunda ni ban taba aikin jarida a baya ba. A sakamakon haka akwai abokaina wanda mu ke harka da su tunda su ‘Yan Jarida ne muna  irin  harkar  abuida  ya  shafi Indiya tare da su. Irin su Aliyu Sufyan da su Muzammil Ibrahim Yakasai duk ‘yan Jarida ne kuma abokaina ne. To na tambayi shi Aliyu Sufyan a kan ya ya aikin ya ke, ya ya a ke karanta labarai da dai sauransu. Sannan kuma nima a kan kaina ina kallon ‘Yan Jaridan yadda su ke labaran a T.B,  ina  kuma  dan  bibiyar  Radio. A  haka  dai  na  ringa  kulle kaina  a daki ina gwadawa. To Allah cikin ikonsa sai ya taimake ni har na bada abunda a ke bukata.

Zuwa Yanzu Ka Samu Sha’awar Yin Aikin Jarida A Rayuwarka Ta Zahiri Kuwa? Ehh gaskiya na ji dadi da ka yi min wannan tambayar. Kamar yadda na fada maka a baya  gaskiya  kafun  na  zo  shirin Kwana Casa’in ko kadan ba ni da sha’awar aikin Jarida. Amma yanzu kasancewar na yi kuma na ji dadi, kuma ina jin dadi da yadda mutane su ke yabona cewa na kayatar da su, na birge su, suna cewa ina ma na zama dan jarida, sai son aikin ya shiga zuciyata. Don haka yanzu na ji ina son aikin jarida wallahi dari bisa dari.

Shin Ka Na Ganin Za Ka  Iya  Ci-Gaba  Da  Irin Gwagwarmaya  Da  Bibiyar Aikace-Aikacen Gwamnati Kamar Yadda Ka Gabatar A Cikin Kwana Casa’in? Eh to gaskiya zan iya kuma bazan iya ba. Saboda gaskiya akwai kalubale da yawa. Saboda yadda a ka nuna Sahabi a Kwana Casa’in ya na da tsantseni wanda ko rayuwarsa ce zai iya  bayarwa  indai  a  kan  fadar gaskiya ne. Don haka a gaske abu ne mai wahala duba da irin yanayin kasarmu da mu ke ciki. Da  ka  fara  ma  kafin  a  je  ko’ina za  a saka a  kore ka. To  a  yanzu ma  ka  ga  dai  duk  da  cewa  fitowar da  na yi a Sahabi a cikin  shiri  ne ba a gaske ba, amma ina samun barazana sosai. Domin wasu har mahaifina  su  ke  samu  suna  fada masa ka jawa danka kunne wai ina fada da Gwamnati. To su ka ga sun dauki abun ma a gaske. To gaskiya zan iya abinda na yi a shirin sai dai abu ne mai wahala da kuma sarkakiya. Shi yasa nace  maka  zan  iya  kuma  bazan iya ba.

Me  Za  Ka  Iya  Cewa  A  Kan Zargin  Da  Mutane  Da  Yawa Su Ke Yi Na Cewa Shirin Nan Naku Na Kwana Casa’in Kai Tsaye  Yana  Sukar  Akidun Wasu Gwamnatoci Ne A Kasar Nan? To  gaskiyar  magana  shirin Kwana Casa’in ba ya sukar akidar kowacce Gwamnati a wannan kasar. Wannan ne ya sa a kowanne shiri idan za a haska a farkonsa za  ka an rubuta cewa shi fa wannan shiri kagaggen labari ne, idan suna ko yanayi ya yi kama to Arashi ne. Don haka ba maganar sukar wata Gwamnati ko sa ka talakawa tawaye a wannan shirin. Kawai abunda muka dauka shi ne duk inda a ka kai wannan shiri, idan mutum yana aikata irin abinda a ka bayyana a cikin shirin, kawai sai mutum ya dauka da shi a ke musamman idan ya na aikata irin  laifin.  Saboda  haka  kawai nazari a kayi a kan irin abunda ya ke faruwa a cikin rayuwa ta zahiri sai a ka gina labarin a kai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: