Mai karatu, yau muna dauke maku ne da karashen tattaunawar da muka yi da Mataimakin Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa, wanda kuma ya jima a wannan aiki, wato KWAMARED MUKTAR GIDADO (JARMAN ALKALERI), wanda wakilinmu KHALID I. IBRAHIM ya tattauna da shi. Za mu dan koma baya kadan.
Ko akwai wani alfamu da Kwamared Gidado zai iya cewa wannan aiki ya samar masa a rayuwa? “Wallahi kwarai da gaske kuwa. Kai ni a karin farko ma ina godiya ga Allah da ya sanyani na shiga wannan aiki na jarida, aikin nan ya bude min idanu na shiga kasashe da yawa, na je kasashen duniya sun fi goma a sanadiyyar aikin jarida.
A dalilin wannan sana’ar na san manyan mutane, jama’a da daman gaske, basira, daukaka duk wannan abin na yi murna da farin ciki ne, kuma dukkaninsu nasara ce a gareni. A lokacin da na ke shugabancin NUJ, ko’ina na je za ka ji ana ‘Ciyaman, Ciyaman,’ wannan daukakar ma kawai nasara ce da Allah ya ba ni. Wajen da ba ka yi tsammanin shiga ba za ka shiga. Martabar da na samu a aikin jarida, gaskiya duk suna daga cikin alfanun da na samu a aikin nan.
Na shiga kasashe sama da goma, kamar su Spain, Kuba, Moroko, Senagal, Saudiyya, Habasha da sauransu. A jihohin Nijeriya kuwa babu wata jihar da ban je sau 3-4 ba a dalilin aikin jarida, jihohin da na shugabanta na Arewa maso Gabas na je su ya fi sau 10-10, wasu ma na je sau 20, wasu 30 dukkaninsu aikin jarida ya kai ni. Na kuma samu damar zuwa hajji da kuma damarmakin da na samu na taimaka ma wasu a aikin nan. Wannan duk nasara ce da alfanu, wannan abin godiya ne a gareni.”
Kai ta kan kai mu sanya sunaye da hotunansu a jaridu da mujallu, muna bayyana cewar wadannan ba mambobinmu ba ne, saboda sun aikata wasu abubuwan assha, sun bata mana aikinmu, sun sanya mutane suna ganin aikin da kaskanci.
To muna kokarinmu, kamar yadda na fada maka a kungiyance, sannan kuma muna da kwamitoci na ladabtarwa din. Amma kokarinmu fa ba zai iyu ba kamar yadda muke fada wa gwamnati a kowane lokaci, sai mun samu dokar da za ta tsara ayyuka da muradu da kuma martabar wannan aikin, fakat, abu guda da muke nema ke nan.”
Ko Gidado yana nufin ana samar da wannan dokar, aikin jarida zai tsaftata ke nan? “Tabbas zai yi sauki sosai, ana samun dokar da za ta sanya cewar kafin ka kafa gidan jarida ga dokokin da za ka bi, ga kuma ka’idojin da za ka cika, kuma idan ka taka doka kaza ne hukuncinka, in ka aikata kaza ga hukuncinka ko ga tararka.
Sannan kuma ba za ka dauki wanda bai kware a aikin jarida ba, ba za ka dauki wanda bai karanci aikin jarida ba, kuma dole ne ka biya ma’aikatanka albashi mai tsoka gwamnati ta yanke. Ai ka san duk abubuwan da suke faruwa din nan wasu ma sabili da yunwa ne.
Yanzu su wadannan gidajen rediyon da ba su da rijista da kuma gidajen jaridun da ba su da rijista din nan, za su dauki mutum ne aiki kawai sai dai ya zo a ba shi I.D Card, ba za su biya shi albashi ba. Kana ba shi, tamkar ka ba shi lasin din ya je ya cuci mutane ne. Idan ba an sanya dokar nan da muke magana ba, gyaran zai yi wahala.
Ya kuma kamata ne a ce gidajen rediyo, telebishin da jaridu suke samar wa ma’aikatansu ababen hawa, kada ka tura mutum dauko labari ba tare da abin hadawa ba; gwamnati ma ya kamata take samar wa gidajen jaridu da motoci.
Sannan da bukatar gwamanati da masu gidajen jaridu masu zaman kansu su samar da wuraren aiki masu kyau, kayan aiki ga ma’aikata, idan aka yi wadannan duk wani ma’aikacin da ya saba dokar aiki kun ga akwai hujjar hukunta shi daidai da laifinsa. Kuma da zarar aka bi wadanan lamarin, to kashi 90 zai ragu, domin na san akwai son zuciya na wasu, amma dai dokar na samuwa komai zai ragu”.
Idan ka je neman labarai, kodayake yanzu Alhamudullah, an sakar mana mara, an samar mana da ‘yancin neman bayanai/labarai ba tare da an musguna maka ba, ‘Freedom of information.’ Wannan dokar mutane ba su gane mata ba ne, ba fa wai kawai ga ‘yan jarida aka yi wannan dokar ba, ga kowane dan kasa ne. Su kuma jama’a sun dauka wai ga ‘yan jarida ne kawai aka samar da wannan dokar. Mai tallan kosai, lebura, mai kwadogo, kowa yana da ‘yancin shiga kowane ma’aikata ya tambayi kaza ko kaza, ka kuma binciki abin da ka ji. To akwai bukatar ‘yan jarida suke amfani da wannan damar wajen bincike da kuma bin bahasin labarai kafin aikin jarida, a rinka tabbatar da yin adalci ga kowane bangare.
Shawarata ga shugabani kuma, ina kira garesu da su tabbatar da kayan aiki ga gidajen jaridu, domin tabbas akwai matsalar kayan aiki. Mu daina yin aikin jarida don nagoro, mu daina amsar kwabo a wajen wasu. Bai kamata kana dan jarida ka sayar da mutuncinka da kimarka a kan Naira Dubu Biyar ko ma kasa da hakan ba. Mu yi aikinmu tsakani da Allah, wata kila Allah ya taimakemu ta wannan fannin.
Daga karshe ina kira ga shugabanni da mu rike gaskiya mu kuma yi hidima don mambobinmu, ba don kanmu ba.
tare da
Muhammad Awwal Umar
email:awalumar7@gmail.com 08093947702