Aikin Mace: Gyara Ko Barna?

Aure yarjejjeniya ce ta zaman tare na iyali, wanda a ke sa ran kwanciyar hankali da nutsuwa cikinta. Babbar ribar da a ke fata da an yi aure shi ne samun iyali. Iyali kuwa nagartattu su ne abin nema, don gina rayuwar al’umma masu tasowa. Mata su ne ginshiki na kula da gida da ma maigidan da ’ya’yan gida da ma duk wani wanda ke mu’amala da gidan.

Mace da ke fita aiki, sawa’un aikin nan na gwamnati ne ko kuma akasin haka, ta na da kalubale, inda wasu ke hangen wannan fita da ta ke yi abu ne na larura da taimakon kai, wasu kuma a hangensu sam mace ta zauna a gida shi ne ma fi a’ala da dacewa.

Don haka duk matar da mijinta ya bar ta aiki ya kamata ta zama kamar haka:-

Kamun Kai

Kamun kai ya na da matukar muhimmanci a gun kowacce mace tun daga kan marar aure bare kuma wadda ta ke ta mallaki hankalinta har ta ke da igiyar aure. A na gane mace marar kamun kai ta hanyoyi da dama ciki akwai:

  1. Surutu barkatai

Za a ga wata matar rau-rau harshenta ya karade ko’ina a wajen aiki, ba a wajen abokanan aikinta mata ba, har a waje mazan ta zama tamkar radiyo. Idan ta fara zuba abinda a ka tambaye ta da ma wanda ba a ma saka ta ba, duk za ta yi uwa ta yi makarbiya.

  1. Ciye-ciye

Duk macen da za ta zama a gaban kowa za ta hau ciye-ciye, to fa ta na da matsalar kamun kai.

  1. Matsattsun Kaya

Sanya sutura mai nuna tsiraici shi ma wani salo ne na nuna rashin kamun kai. Duk mace ta kwarai ya zama wajibi ta sanya sutura wacce za ta rufe jikinta ruf.

  1. Roko

Roko hanya ce ta nuna rashin kamun kai  ga mace. Wasu matan su na da dabi’ar roke-roke a hannun maza, wanda wannan roko shi zai ba da hanyar abubuwa da dama su shigo na raini ko maganar banza.

Gori

Abu na gaba shi ne goro. Maza da dama ba aikin mace ne ba sa so ba, sai dai gudun gori. Akwai matar da duk abinda su ka yi wa miji ko danginsa ko ma yaransu, sai su goranta, wanda wannan ba karamin nakasu ba ne.

Yawo

Wata matar ba ta gajiya da fita. Bayan yarda da mijinta ya yi da ita ya bar ta ta ke fita aikin, kuma sai ta kirkirarwa kanta wani sabon yawon. Ita ce kasuwa, ita ce yawon biki da suna har da ma inda bai dace ta je ba, kuma da aikin za ta fake ta je.

Rashin mayar da hankali ga al’amuran gida

Akwai mata da dama da idan su na aiki kuma sai su kawar da kansu ga duk wani abu na mazajensu kama daga gyaran gida zuwa abinci da ma kula da tsaftar yara da tarbiyyarsu. Akwai wasu matan da idan su na aiki, rayuwar ’ya’yansu da tarbiyyarsu ta koma hannun makwabta ko ’yan aiki, wanda wannan babbar matsala ce ga rayuwar iyali.

Gadara/Wulakanci

Wata matar kuwa don ta ga ta na aiki ta na daukar albashi, sai ta zama tsakaninta da mijinta sai gadara da wulakanci. Hatta dangin miji za ta ke kallon su ba a bakin komai ba. Shi kansa biyayya da Allah Ya wajabta mata ta yi ma sa, sai ta gagara.

Barin wata kafa da za a yi zargi

Sau tari mata su ke barin wata kafa ko su darsawa mazajensu wani abu da zargi zai biyo baya. Misali ta dawo gida da wani abu na abokin aikinta, wanda bai ma shafi aikin ba, ko kuma a dawo gida a shiga yin waya a na hira da wani ko kuma ba da wata kulawa ta musamman.

Wadannan da ma wasu dalilai su ke sa wa maza na tsoro ko kuma su na kyamar mace mai aiki.

Aikin mace na da fa’ida kwarai kuma ba lallai sai ma aikin ba; abin da a ka fi bukata shi ne a samarwa mata abin yi. Akwai sana’oi da mata za su iya aiwatarwa a cikin gidajensu, irin wadanda iyayenmu da kakanninmu ke yi kuma sun yi rayuwa mai kyau sun amfani kansu sun amfani wasu.

Mace idan ta na aiki ya kamata ta zama mai nutsuwa da sanin ya kamata da kyautatawa. Duk abinda mace za ta yi ta fara sa tsoron Allah a gaba ta tsayar da hakkin Allah. Duk matar da mijnta ya bar ta ta yi aiki ko sana’a, to fa ya wuce gori ko wulakanci ko rashin biyayya, don zalunci ne saka alkhairi da sharri.

Hakkin maigida ne daukar dawainiyar dukkan gidansa, amma kyautatawa ce idan ki na aiki ki taimakawa maigida ko da kuwa ya na da shi. Kada ki sa ido a al’amuransa, sannan ’yan uwansa ki kyautata mu su. Wannan alamu ne na tukwici ga abinda dan uwansu ya yi miki na barinki ki nemi naki na kanki.

Ku kuma me ku ka ce kakan aikin mace? Al’umma kowa da hangensa. Bari mu ji me su ka ce:

Rahma Kabir

Mace Mai fita aiki ta fi ba wa ’ya’yanta tarbiyya. Hujja? Saboda ta na da ilimi da kuma abin hannu da za ta kawar da idon ’ya’yanta a kwadayi. Maza sun sakarwa mata harkokin gida. Idan har ta zama cima zaune, to fa zaman ma ba zai yi wu ba. Sannan mutuwa na iya giftawa; yaran nan in har uwa ba ta da abin yi, zai yi wahala ta iya daukar ragamar yaran wanda a karshe rushewar tarbiyya da ma gidan bakidaya ya zo kenan.

Fulani Hafsat

Ilimi shi ne gishirin zaman duniya. Mace da ke fita ta na da damar samun ilimi na zaman rayuwa bayan ilimi da ta samu na Boko ko Arabiya. Mace mai wannan ilimin ta na koya wa yaranta zaman duniya da kyakkyawar mu’amala.

Asama’u Lamido

Idan har za a yi magana ne bisa doron gaskiya, to fa mace mai zama a gida da yaranta sun fi samun tarbiyya da kulawa, don kuwa iyayenmu ba su yi ilimin bokon ba, ba sufita ko’ina ba, amma sun ilmantar da yara. Hatta kallo da ido idan uwa ta yi wa d anta, ya san ma’anarsa, saboda tsabar tarbiyya. Uwa ita ce makarantar farko ta da. Ta jikinta ya ke samun dukkan matakin nasara. To, idan haka ne, wacce uwa ce ma’aikaciya ta ke da wannan cikakken lokacin na zama da yaran?

Ummy Abdul

Mace mai fita aiki ta fi samun dace wajen sa’ar zama lafiya gidan mijinta.

Hafsat Bashir

Addini ma cewa ya yi mata su zauna a cikin gidajensu. Don haka babu wata hujja da zai sa mace ta fita kwadago. Ai ma fitar da mata su ke yi ne ya janyo mazan su ka sangarce su ka sarayar da hakkinsu, amma da mata za su yi zamansu cikin gida, dole a nemo a ba su. Don haka ni dai na fi ganin mata su daina zuwa aiki, su yi zamansu su kula da mazajensu da ‘ya’yansu.

Allah ya kawo ma na dauki da zaman lafiya a gidajenmu. Sati mai zuwa za mu tattauna a kan matsalolin da mata masu aiki ke fuskanta a gidajensu da ma wajen gidan in sha Allahu.

Exit mobile version