Wani mummunan hatsarin mota daya afku a lardin Asir da ke kudancin kasar Saudiyya, ya ci rayukan mutane 20 a yayin jigilar masu aikin Umara zuwa garuruwa mafi tsarki a kasar Saudiyya – Makkah da Madina.
Hakan dai ya zo ne a cikin makon farko na watan Ramadan, lokacin da ake gudanar da aikin umrah, kuma watanni kadan ya rage miliyoyin al’ummar Musulmi su yi aikin hajjin bana a kasar mai tsarki.
Tashar talabijin ta Al-Ekhbariya da ke da alaka da gwamnati ta rahoto cewa, “A cewar bayanan farko da muka samu yanzu, adadin wadanda suka rasu a hatsarin ya kai 20, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai kusan 29.”
Ya ce wadanda abin ya shafa ” ‘yan kasashe daban-daban ne” amma ba a riga an tantance bayanansu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp