Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ta kasar Sin ta fidda bayani a jiya Talata cewa, cikin rabin farkon shekarar bana, yawan zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ya kai ton-kilomita biliyan 78.35, adadin da ya karu da kaso 11.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Kana, yawan zirga-zirgar fasinjoji ya kai miliyan 370, wanda ya karu da kaso 6 bisa dari. A sa’i daya kuma, yawan zirga-zirgar hajoji da kunshin kayayyaki ya kai ton miliyan 4 da dubu 784, wanda ya karu da kaso 14.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Cikin taron aiki da hukumar zirga-zirgar jigaren sama ta fasinja ta kira a jiyan, shugaban hukumar Song Zhiyong ya bayyana cewa, an gudanar da aikin tsaro yadda ya kamata, ganin aikin zirga-zirgar jiragen sama ya karu da kaso 5.6 bisa dari cikin rabin farkon bana, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara.
Haka zalika, a rabin farkon na bana, tsawon lokacin zirga-zirgar jiragen sama na gama gari ya kai awoyi dubu 570, kana, yawan jiragen sama marasa matuki da jama’ar kasa suka yi rajista ya kai miliyan 2 da dubu 726. Lamarin da ya nuna cewa, harkokin zirga-zirgar jiragen sama ta gama gari, da tattalin arzikin jiragen saman dake zirga-zirga kusa da doron kasa, suna bunkasuwa bisa tsari. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp