Mustapha Ibrahim" />

Aikinmu Horar Da Masu Bukatar Bashin CBN–Shugaban Danrabi Global

Aminu Abubakar shi ne shugaban Cibiyar Danrabi A Global Nigeria LTD, wanda kuma shi ne ya jagoranci hurar da matasa maza da mata Dabarun sarafa kudi Dan bunkasa harkar Noma Da Kiwo da kuma yadda mutum zai rubuta bayanin yadda zai gabatarda noma ko kiwo shi ne aikin su a wannan Bita ta kwana biyar amma ba su ne masu bada bashin ba, CBN ne masu bawa wanda ya samu wannan Horo bashi mutokar ya samu Takar dar shaidar wannan Horoin ya cika shardan da mu ke bayarwa.
Alhaji Aminu Abubukar ya bayyana haka ne a lokacin bude Bita da a kayi a Gidan Tunawa Da Malam Aminu Kano da ke Gwammaja cikin Birnin Kano.
Har ila yau Aminu Abubakar ya shawarci alumma da su tsaya su dage su cika kaidar da CBN Dan sa mun wannan Bashi da zaka iya yin Noma,kiwon Shano,Kaji ko kifi, abun da ba`a yadda ba shi ne ka karbi bashin ka yi Aure ko Gini, kuma yana da kyau matasa su dage su Biya Kudin wannan Bita ko Horo a duk inda za a yi kada mu yarda a barmu a baya mu shiga domin samun bashin CBN ta Bankin Nirsal Micro Finance wato kana nan Bankuna da aka kafasu kamar dai yadda Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tsara haka acewar shugaban danrabi Global.

Exit mobile version