Majalisar Wakilai Ta Ƙasa (NASS) ta yi gargaɗin cewa idan ba a yi taka tsantsan ba, matsayinta na bashin gwamnati, wanda ya kai Naira tiriliyan 149.39 daidai da Dala biliyan (97) a kwata na farko na shekarar 2025, na iya haifar da haɗari ga makomar ƙasa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ne suka yi wannan gargaɗin a taron shekara-shekara na 11 a babban taro na Ƙungiyar Kwamitocin Binciken Asusun Jama’a ta Yammacin Afirka (West Africa Association of Public Accounts Committees – WAAPAC) da aka gudanar a Abuja jiya.
- Akpabio Ya Ƙaryata Jita-jitar Ba Shi Da Lafiya
- Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatun Akpabio Kan Dakatar Da Sanata Natasha
Taron shekara-shekara an shirya shi ne ta Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Wakilai, mai taken: “Ƙarfafa Kula da Majalisa kan Bashin Gwamnati.”
Akpabio, wanda Sanata Osita Izunaso, shugaban Kwamitin Kasuwar Hannayen Jari na Majalisar Dattawa ya wakilta, ya bayyana cewa rashin kulawa da bashin gwamnati na iya sanya makomar ‘yan ƙasa cikin haɗari kuma ya raunana dimokuradiyya a faɗin yammacin Afirka.
Ya bayyana cewa kulawar majalisa ba za ta yi watsi da lamarin wajen tabbatar da daidaiton kuɗaɗen gwamnati ba, kuma idan aka sarrafa bashin yadda ya kamata, zai zama muhimmin aiki wajen ɗaukar nauyin ayyukan more rayuwa, da ci gaban ɗorewa.
Akpabio ya yi kira ga duk ƙasashen membobin WAAPAC da su samar da izinin majalisa ga kwamitocin da suka dace, yana mai cewa hakan zai tabbatar da ‘yancinsu da ingancinsu wajen kare dukiyar jama’a.
“Bashin gwamnati, idan aka sarrafa shi yadda ya kamata, zai zama aiki ne mai muhimmanci wajen ɗaukar nauyin ci gaba, ayyukan more rayuwa, da ci gaba mai ɗorewa. Amma idan aka bar shi ba tare da sanya ido ba aka ɓoye shi cikin rashin gaskiya, zai zama nauyi da ke sanya makomar ‘yan ƙasa cikin haɗari.
Wannan shi ya sa majalisa ba za yi watsi da sanya ido a kansa wajen bashi kulawa ba.
“Kwarewar Nijeriya ta nuna cewa idan kwamitocin majalisa suka samu ikon doka, gaskiya da riƙon amana sun ƙaru, kuɗi ya yi ƙarfi, to dimokuraɗiyya ta ƙara inganci,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, Abbas ya gargaɗi cewa basussukan Nijeriya sun kai wani matsayi mai hatsari, inda ya buƙaci majalisun dokoki a faɗin Yammacin Afirka su ƙarfafa sa ido kan aro na gwamnati domin kare makomar ‘yan ƙasashensu.
Da yake magana a madadinsa, Jagoran Majalisar Wakilai, Hon. Julius Ihonɓbhere, Abbas ya bayyana cewa jimillar basussukan gwamnatin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39 (kimanin Dalar Amurka biliyan 97) a zangon farko na shekarar 2025, wanda ya nuna ƙaruwar ta yi tsanani daga Naira tiriliyan 121.7 a shekarar da ta gabata.
Ya bayyana damuwa kan matsayin bashin da aka kwatanta da GDP, wanda a halin yanzu ya kai kusan kashi 52 cikin 100, sama da iyakar kashi 40 cikin 100 da doka ta ƙayyade.
Ya ce: “Wannan karya haddin bashi ne luma hakan wata alama ce ta matsin lamba ga ɗorewar tattalin arziki. Hakan ya nuna gaggawar buƙatar ƙarfafa sa ido, yin aro cikin gaskiya da bayyana dukkan bayanai, da kuma samun haɗin kai domin tabbatar da cewa kowace Naira da aka aro ta samar da ainihin amfanin tattalin arziki da zamantakewa.
“A duk faɗin Afirka, matakin bashi ya kai wani mummunan matsayi. A shekarar 2022, jimillar bashin ƙasashen nahiyar ya kai Dala tiriliyan 1.8, inda bashin wajen shi kaɗai ake sa ran zai zarce Dala tiriliyan 1 a shekarar 2023.”
Ya ce: “Ƙasashe da dama yanzu suna cikin mummunan yanayi na cin bashin da aka kwatanta da GDP: misali; Sudan na da kaso 344, Angola kaso 136.8, Ghana 84, Kenya kusan 70, yayin da Afirka ta Kudu ta haura kaso 77.”
Kakakin majalisar ya lura cewa a faɗin Afirka, bashi ya zama matsalar tsarin tattalin arziki, inda ƙasashe da dama ke kashe kuɗi fiye da na kula da lafiya da sauran muhimman ayyuka wajen biyan bashin da suka karɓa.
A cewarsa, kashi 35 na bashin na ƙasashen Turai ne na masu ba da rance masu zaman kansu, kashi 39 na ƙungiyoyin haɗin gwiwa irin su IMF da Bankin Duniya, kashi 13 kuma na ƙasashen da ke bayar da rance kai tsaye (bilateral creditors), sannan kashi 12 daga Ƙasar China.
Abbas ya ce Nijeriya ta ƙuduri aniyar jagorantar kafa tsarin duba bashin ƙasashen Yammacin Afirka ta majalisar dokoki ƙarƙashin WAAPAC, domin daidaita rahotannin bashi, samar da ƙa’idojin yanki kan gaskiya da bayyana bayanai, tare da bai wa majalisu damar samun bayanai cikin lokaci don inganta bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp