Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa gayyatar kwararru don bayyana bayanai kan sabbin dokokin gyaran haraji wata hanya ce mai kyau da ya kamata a bi.
Ya ce bayan sauraron kwararrun, ‘yan majalisa da jama’a za su fahimci muhimmancin goyon bayan waɗannan dokokin. Ya gode wa mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau, da kuma Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abass, bisa shirya tarurruka don tattaunawa kan hanyoyin inganta tsarin haraji.
- Dambarwar Shirin Tinubu Na Yi Wa Dokar Haraji Kwaskwarima…
- Dokokin Gyaran Haraji Sun Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
Da yake karɓar shugabannin ƙungiyar Sarakunan Niger Delta (ANDMON) a ofishinsa, Akpabio ya yaba wa Sarakunan bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Niger Delta, wanda ya ƙara samar da ywan mai ga Nijeriya. Ya ce akwai buƙatar samar da manufofi masu ƙarfi domin hana gurɓacewar muhalli da ɓarnar kamfanonin mai a yankunan hakar mai. Har ila yau, ya jaddada ƙudirin gwamnati na tsaftace Ogoniland da kammala hanyar East-West don amfanin al’ummar yankin.
Shugaban ANDMON, Captain Okurakpot, ya nuna gamsuwarsu da shugabancin Akpabio, yana mai cewa sun zo domin bayyana goyon bayansu da kuma neman haɗin gwuiwa wajen magance matsalolin tsaro da samar da ayyukan yi ga matasa. Ya ce ƙungiyarsu za ta iya taimaka wa gwamnati wajen inganta samar da mai da kuma shigar da fasahohin wutar lantarki daga hasken rana da iska, domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Niger Delta.