Connect with us

LABARAI

Akume Ga Ortom: Digirin Digirgir Dinka Na Bogi Ne

Published

on

Sanata mai wakiltan mazabar Benuwe ta Arewa, George Akume, da Gwamnan Jihar ta Benuwe, Samuel Ortom, sun yi cacar baki a ranar Litinin.

Akume, wanda ya zargi Gwamna Ortom, da rashin tabuka komai, sannan kuma ya kira shi da wanda yake dauke da digirin digirgir din bogi, a wani taro na masu ruwa da tsakin Jam’iyyar APC wanda aka yi a, cibiyar yin taruka ta, Castle Ebent Centre, da ke Makurdi.

Akume ya zargi Gwamna Ortom da tafiyar da al’amurran Gwamnatin Jihar tamkar wani kayan gidan su, ya fusata da cewa, tilas ne su kore shi daga mulkin Jihar a shekara mai zuwa.

Akume, yana mayar da martani ne kan wata tattaunawan da Gwamna Ortom ya yi da jaridar Punch, Akume ya ce, “Ortom ya ce, ya yi karatunsa na PhD ne a Jami’ar, Commonwealth Unibersity da ke Berlin, amma sam ba wata Jami’a ma mai suna haka. Akalla, ni na yi digiri di na ne na daya da na biyu a Jami’ar Ibadan, ina kuma da digirin girmamawa daga Jami’ar Jos.

“Ya kuma ce, ni jami’i ne mai lura da ayyuka, a lokacin da shi yake a matsayin Shugaban karamar hukuma, wai na ma yi aiki a karkashin sa, ni ban taba ganin Ortom a gidan gwamnati ba a wannan lokacin.

“Ya kuma ce, wai ni ban taba cin wani zabe ba, amma ai na ci zabe a shekarar 1999, a lokacin da shi yake a Jam’iyyar SDP, hakanan a shekarar 2003, lokacin da na koma Jam’iyyar ANC, na sake cin zabe, amma a zabe na baya-bayan nan, Ortom ya fadi ne a karamar hukumarsa. A lokacin da nake gina Jam’iyyar PDP, Ortom yana ina ne?” Akume ke tambaya.

Akume kuma ya zargi Ortom da zagin Shugaba Buhari a kowane lokaci.

Ya kuma kalubalanci gwamnan da ya biya dimbin basukan da ma’aikata da ‘yan fenshon Jihar ke bin sa, domin suna ta mutuwa saboda yunwa.

Amma da yake mayar da martani a madadin Shugaban sa, mai baiwa Gwamna Ortom shawara kan harkokin manema labarai da yanar gizo, Tahaz Agerzua, ya kwatanta Akume da cewa, mashayi ne kawai, wanda bai ma kamata a tsaya kula shi ba.

Agerzua ya ce, ai samun digirin PhD ba shi ne sharadin zama gwamna ba, ya kwatanta sukan da Akumen ya yi a kan haka da dubara ce ta neman kawar da hankalin al’umma.

Mai taimaka wa gwamnan ya yi mamakin, ko yaushe ne Akume ya zama wani mai kimar da har za a tanka masa, sai ya kalubalance shi da ya bayyana wa al’umma aikin da ya yi masu a Majalisan ta Dattawa.

“Kowa ya san Akume mashayi ne kawai, duk cikin maye yake fadin abin da duk yake fada, shi ba wanda za a saurara ne ba.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: