A yayin cin zarafin malaman makakarantun Boko da wasu iyayen dalibai da wasu ‘yan uwan daliban Nijeriya ke yi, wanda lamarin ke ci gaba zama ruwan dare, kawai saboda malaman, sun hukunta ‘ya’yan kan wani laifi da suka aikata a makarantun su, domin yaran su zamo na gari, amma lamarin, bai isa ga kafafen yada labarai.
Wannan rashin isar cin zarafin na su ga kafafen yada labaran, ya sanya, malaman da irin wannan lamarin ya rutsa da su, ke ci gaba da jurewa, su kuma yi gum, da bakinsu, ba tare da sun gayawa kowa ba.
Irin wannan cin zarfin, ya faru hatta a kan Mista Aledander Rotifa wanda Mataimakin Shugaban Kwalejin Complete Child Debelopment College ne, da ke a yankin Aule, karamar hukumar Akure ta Arewa North jihar Ondo, a ranar 26 ga watan Mayun 2025, inda aka yi zargin wata uwa madam Dorcas Asije, mahaifiya ga wani dalibi sun yi hayar wasu bata gari sun ci zarfin Aledander.
Dorcas ta aikata wannan ta’asar kan Aledander ne, don kawai ya kwace wayar salular danta a Kwalejin, a yayin don kar ya aikata magudin jarrabawar WASSCE.
Hakan ya sanya Dorcas tare da wani yayanta wanda tsohon dailibi ne a Kwalejin suka je Kwalejin suka yiwa Aledander barazanar aikakata masa ta’asar na ko dai ya kyale danta ya tabka magun jarrabawar da wayar ta sa, da yake zana darasain lissafi.
Kazalika barazanar ta su bata tsaya nan ba, domin a lokacin da Aledander ke a wani ofishin ‘yansanda, nan ma su bishi har can, tare da bata garin da ta yi haya, inda ta mamayi, wata motar ‘yansandan da ke dauke da Aledander, suka fito da shi waje, suka lakada masa na Jaki.
Sai dai, gwamnatin jihar, ta yi hanzarin shiga lcikin lamarin, inda ‘yansanda, suka cafko Dorcas tare da wasu mutane biyar da ake zargi, suna da hannu, wajen aikata ta’asar.
Kazalika, an gurfanar da su a gaban Kuliya, kan tuhumar hada baki, cin zarfi, barazana ga rayuwarsa, tayar da hayaniya a cikin alumma da kuma yunkurin kisan kai.
Amma mai makon wadanda ake zargin, su nuna damuwa kana abinda ake zargin su, tare da kuma gargadin dan nasu, sai kawai majin Dorcas Mista Elisha Imoukhuede, ya buge da rubata takardar korfi, a kan Aledander da kuma a kan ofishin ‘yansanda na gunduma Okuta Elerinla, zuwa ga Babban Sifetan ‘yansanda.
Bugu da kari, a ranar 12 ga watan Okutobar 2021, ‘yansanda sun kama wani uba mai suna Abidemi Oluwaseun mai shekara 35, kan zargin kutsawa cikin Kwalejin mata ta Baptist Girls’ College, da ke a yankin Idi-Aba a garin Abeokuta na jihar Ogun da wasu bata gari, da ya yi hayarsu, suka ci zarafin wani malamin makarantar, saboda kawai, ya zane ‘yarsa, mai shekaru 15 da bulala,
Hakazali, a ranar 16 ga watan Nuwambar 2021, wani dalibain jami’ar Ilorin mai suna Salaudeen Waliyullah Aanuoluwa, ya lakadawa malamar da ke koyarwa a jami’ar, mai suna Madam Zakariyyah duka, inda har ta kai ga, ta suma.
Duka cikin watan na Nuwambar 2021, iyayen wata dalibar makarantar Jericho High School da ke a Ibadan, sun yo hayar wasu bata gari, suka lakadawa wasu malaman makarantar duka
Haka a ranar 13 na watan Fabirairun 2025, mahukutan jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke a Awka, a jihar Anambra, sun kori wadi dalibi, mai suna Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, bisa cin zarafin wani malamin jami’ar Dakta Chukwudi Okoye, saboda ya dakatar da ita, daga daukar bidiyo ta hanyar kafar TikTok wanda malamin, ya dakatar da ita.
Kazalika, wani malami a wata makarantar kudi a yankin Abrakaa jihar Delta, a ranar 2 na watan Disambar 2021, ya gamu da ajalisan, bayan da ya sha na Jaki, a hannun wani dalibinsa.
Duba da irin wadannan ayyukan na ta’asar, kan malamai, matsayin mu a wannan Jaridar, muna ganin, ga dukkan alamu, batun duk wata kima da malamai ke da ita, ta fara gushewa, musamman duba da yadda a yanzu, girmama na gaba a tsakanin wasu matasa dalibai, ta kau.
Wani karin babban abin takaicin shi ne, yadda wasu iyaye, ke marawa ‘ya’yansu baya, wajen aikata, manyan laifuka, musaman yadda iyayen ke yin uwa da makarbiya, domin ya’yansu, su aikata magun jarrabawa.
Baya ga wannan, wasu iyayen ma, goyawa ‘ya’yansu baya suke yi, domin rungumar damfarar ta yanar Gizo, da aka fi sani da “yahoo”, domin su zamo masu kudi, a dare daya, wanda kuma an sha ruwaito irin wadannan ‘yan Yahoo, har tsafi da rayukan mutane suna yi, bisa nufin neman sa’a.
Ba wai kawai, an kafa makaranta, domin koyar wa bane, ta kuma kasance, waje ne, na koyar da tarbiyya, amma abin bakin ciki, wasu iyayen dalibai, sun kasance suna yin zagon kasa, maimakon su kara karfafa koyar da da’a a tsakanin ‘ya’yansu daliban.
Ko da yake dai, akwai wasu makarantun, da har yanzu, suke ci gaba da yin kokari wajen dakile cin zarafin da wasu daliban, ke yiwa malamansu.
Muna bayar da shawarar cewa, dole ne, a rinka kare rayuwar malamai yayin da suke kan aikinsu na koyar wa.
Kazalika, muna shawartar ‘yansanda, da su tabatar da an gaggauta daukar mataki, kan lamarin da ya auku na Ondo, musamman domin hakan, ya zama izina ga sauran masu tunanin sake aikata haka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp