Kungiyar Manyan Dillalan Mai ta Kasa, MOMAN, ta ce kayyade farashin litar man fetur kan N165 ba tabbataccen abu ba ne.
Olumide Adeosun, shugaban MOMAN, ne ya bayyana haka a ranar Laraba yayin wani taron karawa juna sani na kariya ga masu siyan mai da Hukumar Kare Cinikayya da Sayen ta Tarayya, FCCPC.
Adeosun, wanda ke tsokaci kan matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a fadin kasar, ya dora alhakin lamarin kan rikicin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine, wanda ya kawo cikas ga rarraba makamashi a fadin duniya.
Shugaban MOMAN ya kwatanta halin da ake ciki a halin yanzu da na lokacin annobar Korona, inda wasu kasashe suka yi yunkurin dakatar da fitar da man fetur zuwa kasashensu na samar da makamashi na kasa.
Ya ci gaba da cewa zai yi wahala a tilasta duk wani nau’in tsarin kula da farashi a kan ‘yan kasuwa, wadanda sai da su ka yi hobbaasa daidaita farashinsu dangane da yadda suke siyan kayayyakin daga rumbunan mai.
Shugaban MOMAN ya ce hanyar da za a bi ita ce gwamnati ta gaggauta daukan matakin janye tallafin mai domin a saukaka wa masu sayen a kasar.