Daga Zubairu M Lawal,
Mataimakiyar Sakataren majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad, ta bayyana akwai bukatan matasa su zama masu jajircewa wajen gina Nijeriya domin zama ingantacciya a kasa.
Hajiya Amina Muhammad ta bayyana hakan ne a lokacin, da ta ziyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Nijeriya ta na bukatar tsayayun matasa da za su iya tafiyar da tsarin Gwamnati ta hanyar da komai zai sauya domin samun cigaba mai daurewa.
ya kamata Gwamnati ta samar da ayyukan yi na bunkasa matasan kasarta saboda nan gaba zasu zamo abin koyi wajen bun kasa tattalin arzikin kasa.
Mataimakiyar Sakataren tace akwai ayyukan yi da dama da matasa maza da mata wadanda sukayi karatu dama akasin haka zasu rungume shi wanda zai inganta rayuwar su, da matsayin su a idon Duniya.
Ta ce Ko wata kasa a Duniya ta na alfahari da matasanta wajen gudanar da kere -kere kan kimiyya da fasaha saboda daga darajar kasar bai kamata a ce matasan Nijeriya sun dauru a kan wata hanya ta daban ba.
Samar da ayyukan yi ga matasa hada karfi ne tsakanin matasa da Gwamnati wajen jajircewa domin gina kasa da tattalin arzikin kasa.
Majalisar Dinkin Duniya tayi Allah wadai da abubuwan da suka faru a lokacin zanga zanagar” mu na masu ba ku shawara da ku rungumi matasan kasar ku wajen azasu kan tubalin cigaban ”
Ta kuma shawarci Gwamnati da Kaman ta gaskiya da yin adalci tsakanin matasa da bin hakin wanda aka yiwa ba daidai ba.
A nasa jawabin Shugaban kasa Muhammad Buhari ya jaddada aniyarsa na bunkasa rayuwar matasan Nijeriya zuwa ga tudun mun tsira.
Ya kara da cewa akwai ayyukan cigaba mai taren yawa da Gwamnatin sa ta farfado da shi domin magance zaman kashe wando da matasa keyi a kasa.
Dubban matasa ne suka amfana da wannan shirin na kawar da zaman kashe wando wanda ya kan rage masu radadin talauci.
Ya kara da cewa akwai shirin da Gwamnatin sa takeyi na tattaki karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikata Ibrahim Gambari domin kewayawa fadin kasa dan tattaunawa da masu fada aji da kuma Sarakunan Gargajiya, domin jin ra’ayinsu da magance matsalolin matasa.
Gwamnatin sa kullun tunanin yadda za a bunkasa cigaban matasa da samar masu da ayyukan yi saboda Nijeriya ta na da matasa dayawa da suke zaune babu aikin yi.