Dan wasan gaba na Newcastle Anthony Gordon na daga cikin matasan yan wasan da magoya bayan kasar Ingila, ke fatan ganin koci Gareth Southgate ya saka a cikin yan wasa 11 na farko a wasan da Ingila zata kara kasar Slovekia.
Tsohon dan wasan na Everton, yayin wata hira da ya yi da ‘yan jarida ya bayyana cewar akwai bukatar kasar Ingila ta yi kokarin lashe wannan kofi na Euro duk da cewar akwai wadanda ke ganin ba za su iya ba.
- Sin: Hada-hadar Sufuri Ta Bunkasa Cikin Watanni 5 Na Farkon Shekarar Bana
- Wang Yi Ya Yi Jawabi A Liyafar Murnar Cika Shekaru 70 Da Fitar Da Ka’idoji 5 Na Zaman Tare Cikin Lumana
Ingila wadda ta kare matakin rukuni a matsayi na 1 da nasara daya da canjaras biyu za ta hadu da kasar Slovakia a wasan zagaye na 16 na gasar, a ranar Lahadi da misalin karfe 5 na yamma a filin wasa na Veltins Arena da ke birnin Gelsenkirchenm.
“A kowane lokaci mutane na bukatar ku yi nasara a kowace fafatawa da kuka buga domin su goyi bayanku, saboda haka idan muna son hakan ya tabbata,kawai muna bukatar mu yi mu ba mutane abin da suke son gani,” inji Gordon.
Dan wasan mai shekaru 23, ya fara buga wa Ingila wasa a watan Maris, kuma ya taka rawar gani sosai a kakar farko da ya shafe a Newcastle, inda ya ci kwallaye 12 tare da taimakawa aka zura 11 a wasanni 48.