Abdulrazak Yahuza Jere" />

Akwai Karancin Wayar Da Kai Game Da Cutar Kwarona

Rayuka

Tun bayan barkewar wannan annoba ta Cobid-19 a wannan kasa, Hukumomi na ikrarin cewa, ‘yan Nijeriya biyu ne kacal suka mutu. Kazalika, har izuwa lokacin da aka kammala rubuta wannan rahoto, mutane 190 kadai suka kamu da wannan cuta ta sarkewar numfashi (Coronabirus). Wasu daga cikin ‘yan Nijeriya na kallon wannan al’amari a matsayin wani abu, wanda Allah (SWT) Ya shiga ciki tare da kawo daukinSa, musamman idan aka lura da abinda ke faruwa a sauran sassan kasashen duniya.

Haka zalika, wannan wani abu ne da yake kara yin izina cewa, lallai wannan cuta ba aba ce da ya kamata a yi wasa da ita ba. Sannan, akwai dalilai da ke sake tabbatar da cewa lallai akwai wannan cuta a Nijeriya, duk da dai akwai wadanda ke ganin cewa cutar ba ta illata bakar-fata, wanda kuma ko kadan ba haka al’amarin yake ba.

Babban abin tsoro da takaici a halin yanzu shi ne, yadda wasu ‘yan Nijeriya ke fassara wannan cuta ta Cobid-19 da cewa, wata sabuwar hanya ce wadda mahukunta ke kokarin wawashe dukiyar kasa don amfanin kansu da sunan wannan cuta. A matsayinmu na wannan Gidan Jarida, an fara fargar da mu haka ne lokacin da muka samu kiran waya daga Inugu, ana tambayar mu tare da neman samun tabbacin cewa, ko dai wannan cuta ta Cobid-19 gaskiya ko kuma akasin haka.

A ra’ayin wadda ta bugo mana wannan waya, wadda ta jima da yin Digirinta a Jami’a, sannan a halin yanzu Malamar Sakandire ce, ta yi aure tana kuma da ‘ya’ya shida ta bayyana cewa, ko kadan babu wannan cuta ta Cobid-19 a Nijeriya har ma batun mutane guda biyu da aka ce an rasa tare da bayyana wasu daga cikin Gwamnoni uku da kuma Shugaban Ma’aikatan Babbar Fadar Shugaban Kasa da aka yi, ba gaskiya ba ne. Har kokarin tabbatar mata da hakan da aka yi, amma ko kadan ba ta yarda ba.

Bayan wannan tattaunawa a waya, wani abu guda da wannan Gidan Jarida ya fahimta shi ne, ba a ilmantar da mutane tare da wayar musu da kai a kan wannan cuta ta Cobid-19 yadda ya kamata. Ba ma batun cewa lallai akwai cutar ba, har ma batun illolin da take dauke da su da kuma hanyoyin da ake bi domin kiyaye su. Mafi yawan ‘yan Nijeriya, misali kamar wannan wadda ta yi mana waya daga Inugu, ba su san cewa har yanzu ba a samu maganin da yake warkar da wannan cuta a fadin duniya baki-daya ba, duk maganin da ake amfani da shi yanzu ana yi ne a matsayin gwaji.

Mu a namu tsammanin, musamman ganin yadda wasu daga cikin manyan mutane a kasar nan suka kamu da wannan cuta, zai sa ya zama izina ga Hukumomi wajen daukar kwararen matakai, domin dakile yaduwarta da sauran dukkanin abubuwan da suka kamata, amma sai ga shi hakan bai samu ba. Saboda haka, ya zama wajibi Hukumomi su sake waiwayar wannan al’amari ta hanyar wayar da kan al’ummar wannan kasa illolin wannan cuta da sauran makamantansu, ta hanyar har wadanda ke yawo a kan tituna za su gamsu akwai wannan cuta tare da kiyaye hanyoyin da ake bi wajen kamuwa da ita.

A kaf Jihohin Nijeriya, Jihar Legas ce kadai ta mayar da hankali tare da daukar kwararen matakai kan wannan cuta, amma sauran jihohin babu abinda ya canza hada-hadar neman kudinsu kawai suke yi suna fakewa da cutar, wanda wannan ke sake tabbatar da cewa, Shugabannin Siyasa ko kadan ba su dauki hanyar sauke nauyin hakkin al’ummar da ke karkashinsu ba.

Haka nan, rufe iyakokin kasa na daya daga cikin manyan matakan hana yaduwar wannan cuta, a namu ra’ayin, wannan abu ne da zama wajibi a daidai wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da manya-manyan kasashen da suka cigaba suke kuma da ingantattun kayan kula da harkar lafiya, amma bai hana kusan mutane Milyan daya daga cikinsu sun kamu da wannan cuta ba.

Har ila yau, duk da ganin abinda ke faruwa a kasashe kamar Italiya, Spain, Ingila da kuma Amurka, amma bai zama darasi ga Nijeriya wajen daukar kwararan matakan da suka dace, kamar yadda ta yi bayan barkewar cutar Ebola ba. Kusan baki-dayan Ma’aikatan da suka yi wancan aiki, yanzu sun yi ritaya. Sannan, har yanzu wannan kwarewa tasu ta sanin makamar aiki na nan, da za a sake dauko su ko shakka babu, za su kara nuna bajintarsu tare da yin iyakar kokarinsu wajen bayar da tasu gudunmawar kan wannan cuta ta Cobid-19.

‘Yan Nijeriya sun saba yin watsi da kudi idan wata matsala ta taso, amma a karshe bukata ba ta biya ba, watakila ma sai dai abin ya kara ta’azzara. Don haka, ya zama wajibi Hukumomi su kara zage damtse, wajen aiwatar da abinda ya dace ga al’ummar wannan kasa. Sannan, su ma sauran al’ummar wannan kasa wajibi su yi nasu kokarin domin dakile yaduwar wannan cuta ta Cobid-19.

A karshe, muna sake yin kira ga Hukumomin kasar nan, su takawa ‘yan Nijeriya birki wajen kambamawa tare da kara yawan wadanda ke dauke da wannan cuta ta shafukan sada zumunta da sauran makmantansu.

 

Exit mobile version