Wata ƙungiyar dattijan jihar Zamfara ta zargi Gwamna Dauda Lawal da yin maganganun da ba su dace ba game da ba da magani kyauta ga waɗanda ‘yan bindigar daji suka raunata.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Hon Aliyu Muhammad Gummi, ya ƙalubalanci gwamnan ya nuna shaidar cewa an ba wa waɗanda abin ya shafa magani kyauta a asibitocin jihar, kamar yadda ya yi iƙirari a wata hira ƴan jarida.
- Gwamna Lawal Ya Jaddada Aniyar Inganta Kiwon Lafiya A Jihar Zamfara
- ’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya
“Wannan shi ne mafi girman rashin gaskiya,” in ji Gummi, yana mai cewa gwamnan ya kasa cika alƙawarinsa na yaƙi da ta’addanci cikin watanni biyu da samun mulki.
Ƙungiyar ta yi kakkausar suka kan yadda gwamnan ke yawan balaguro zuwa ƙasashen waje yayin da jama’a ke fama da matsalar ta’addanci, inda ya ce:
“Ya kamata ya dakatar da waɗannan tafiye-tafiye ya maida hankali kan matsalolin jihar.”
Tsofaffin sun yi kira ga ‘yan jarida da su tabbatar da iƙirarin gwamnan cewa ana ba wa waɗanda aka harba a yankuna masu nisa kamar Tsafe magani kyauta, tare da buƙatar a wallafa sunayen waɗanda aka biya musu magani da shaidun biyan kuɗi.
“Mutanen Zamfara ba wawaye ba ne. Gwamnan ya kamata ya daina waɗannan maganganun ƙarya, ya daina farfaganda, ya kuma haɗa kai da masu ruwa da tsaki na gaskiya don magance matsalar tsaro,” in ji Gummi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp