• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Ma’ana Mai Zurfi A Bayan Da’a

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Ma'ana

Ranar 25 ga watan Mayu, rana ce ta “Ranar Afirka”, wato ranar tunawa da kafuwar Kungiyar Hadin Kan Afirka, wadda daga bisani ta zama Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU. A jiya Litinin, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da daukacin jakadun kasashen Afirka da ke kasar Sin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda suka gudanar da bikin murnar wannan rana mai ma’anar musamman ga Afirka. Wannan ya nuna abokantaka da ke tsakanin Sin da Afirka, tare da shaida yadda mutanen Sin da Afirka suke dora muhimmanci kan da’a.

‘Yan Afirka, kamar Sinawa, suna mai da hankali sosai ga da’a. A duk lokacin bukukuwa, na kan samu kiran waya da gaisuwa daga abokai ‘yan Afirka da yawa. Ina ganin za su iya fahimtar muhimmancin bikin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya shirya a wannan karo, da sauran abubuwan da suka nuna yadda jama’ar kasar Sin suke daukar da’a da muhimmanci, misalin ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan kai Afirka a farkon kowace shekara.

  • Gwamnati Ta Kammala Samar Da Fasfo Sama Da 200,000 Da Suka Yi Jinkiri
  • Tsarin Dunkulewar Aiki Ba Da Ilmi Da Kimiyya Da Kwararru Na Sin Ya Dace Da Yanayin Zamani

Da’a ba ta shafi “al’ada” kawai ba, tana kuma wakiltar ka’idoji da dabi’a, da dorewar huldar mutane da ta kasa da kasa. Kamar dai wannan biki na tunawa da “ranar Afirka”, wanda ya tattaro wakilan Sin da Afirka, don waiwayar yadda jama’ar Sin da ta Afirka suka nuna goyon baya ga juna a fafutukar kare ikon mulkin kasa, da kuma taimakawa juna a kokarin farfado da al’umma, tare da alkawarin ci gaba da kokarin hadin kai a nan gaba. Wannan yanayin hulda mai dorewa yana baiwa mutane damar mai da hankali kan tsare-tsaren ci gaba na dogon lokaci, da kuma neman inganta dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashe a kai a kai. Kasar da ke da da’a da mutunci ba za ta taba kaddamar da yakin haraji kan kasashen duniya ba, saboda ta fahimci darajar kwanciyar hankali da yanayin tabbaci ga ci gaban wata kasa da na al’ummarta cikin dogon lokaci.

 

Da’a da dabi’a sun shafi mutunta juna, wanda shi ne abin da ake bukata don samun sakamako mai gamsarwa ga dukkan bangarorin da suke hadin gwiwa da juna. Saboda tana mutunta kasashen Afirka, kasar Sin ta iya daidaita yadda ake rarraba moriya a hadin gwiwar da ke tsakaninta da Afirka, da kuma ba da karin goyon baya wajen biyan bukatun raya kasashen Afirka. Misali, a shekarar 2024, kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga Afirka sun karu da kashi 6.9%, wanda ya zarta karuwar kashi 3.5% na kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen Afirka. Ban da haka, yankunan ciniki cikin ‘yanci na Lekki, da na Ogun-Guangdong da kamfanonin kasar Sin suka zuba jari a cikinsu, da gina su, da sarrafa su a Najeriya, sun samar da guraben ayyukan yi sama da 20,000 ga al’ummar Najeriya, tare da jawo jarin kimanin dalar Amurka biliyan 2.6. Wadannan misalan sun nuna irin kokarin da kasar Sin ke yi na inganta hadin gwiwa mai amfanar juna tare da kasashen Afirka. Ba kamar a wata kasa ta daban ba, inda aka tilastawa shugaban wata babbar kasa ta Afirka da ya yi hakuri da tsokana, da wulakanci a gaban daukacin jama’ar duniya baki daya. Irin wannan kasa bata ganin komai sai karfi kadai, tana son cin moriya da faduwar wani, kuma ba ta san da’a da mutunci, da yiwuwar samun ci gaba na bai daya ba.

LABARAI MASU NASABA

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

 

Tabbas a halin yanzu, wasu kasashe ba su ba da’a muhimmanci ba, kana suna ta daukar matakan kashin kai yadda suka ga dama, lamarin da ya sa al’amuran kasa da kasa suka shiga rudani. Dangane da wannan batu, dole ne Sin da kasashen Afirka masu da’a su karfafa hadin kai, su yi adawa da siyasar nuna fin karfi, da daukaka ra’ayin cudanyar mabambantan bangarori masu fada-a-ji a duniya, da kare tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya. Ta la’akari da yadda adadin yawan al’ummar Sin da Afirka ya kai kashi daya bisa uku na yawan al’ummar duniya, kokarin hadin gwiwarmu tabbas zai karkata duniya zuwa ga turba mai dacewa. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Ra'ayi Riga

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ra'ayi Riga

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Next Post
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Amso Bashin $21.5bn Da ₦757.9bn

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.