Daga Muhammad Sani Chinade, Damaturu
LEADERSHIP A Yau ta samu tattaunawa da wani matashi dan kimanin shekara 26 da ke sana’ar sayar da magungunan zamani Yusuf Muhammad Lamsha Potaskum a Jihar Yobe wanda a yanzu haka ya mallaki kantunan sayar da magunguna na zamani Kemis guda biyu wadanda ya ce, sana’ar sayar da magungunan zamani ta yi masa komai na rayuwa.
LEADERSHIP A YAU: Yaushe ka fara gudanar da wannan sana’a taka ta sayar da magungunan zamani (medicine), kuma ta yaya ka fara?
LAMSHA: To alhamdu lillah na fara sana’ar sayar da magungunan zamani ne tun a shekarar 2005 wato tun ina dan shekara 15 ke nan kuma na fara ne da kasa magungunan a cikin kwando ina yawo kwararo-kwararo daga bisani kuma na fara zuwa kasuwanni.
LEADERSHIP A YAU: Bayan kantuna biyu da ka bude, shin ko akwai wasu karin nasarori da ka cimma da kake fahari da su a kan wannan sana’a?
LAMSHA:.Alal hakika na cimma karin nasarori na rayuwa da nake fahari da su dangane da wannan sana’a ta sayar da magunguna, domin bayan shagunguna biyu da na bude cike da magunguna na kuma gina gidan kaina na yi aure na sa amaryar ciki kana nakan dduki kusan dukannin dawainiyar iyalen gidanmu tare da biyan kudaden makarantar kannena kuma ni kaina ma na dauki dawainiyar kaina da kaina yadda har na je na yi karatun Diploma da ta yi sanadiyar samun aikin gwamnati da sauran dawainiya ta ‘yan’uwa da abokan arziki daidai gwargwadon yadda zan iya. Don haka a gaskiya wannan sana’a ta sayar da magungunan zamani ta yi min komai na rayuwa tabarkallah.
LEADERSHIP A YAU: Da yake wannan irin sana’a taku na bukatar kwarewa da neman izini daga hukuma, shin ko kaima ka bi wannan mataki?
LAMSHA…Alal hakika hukuma ta san da ni don kuma na samu izinin bude kantunan sayar da magani daga gare ta. Kuma batun kwarewa kuwa alhamdu lillah ina da daidai gwargwado.
LEADERSHIP A YAU…Wane kira kake da shi ga masu wannan irin wannan sana’a taka ta sayar da magunguna musamman don bin doka da oda?
LAMSHA.:To ina kira da babbar murya ga ‘yan’uwana dake wannan sana’a ta sayar da magungunan zamani na gefen tituna da masu zama wuri daya a kantuna da a guji ta’ammali da sayar da miyagun kwayoyin da gwamnati ta hana da kuma kwayoyin da amfaninsu ya kare da wadanda ba su da lambobi da sauransu.