Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi ikirarin cewa akwai wasu kusoshin fadar shugaban kasa da ke goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sake duba yadda ake aiwatar da manufar sauya fasalin kudin kasar nan zuwa yanzu domin halin wahala da mutane ke ciki.
- Ya Kamata Amurka Ta Nuna Girmamawa Yayin Sake Bude Ofishin Jakadancinta A Solomon
- Sin Za Ta Fadada Shigo Da Hajoji Masu Nagarta A Shekarar Nan Ta 2023
Wike ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a filin Sakandare na Comprehensive da ke garin Ibaka, a tsibirin Okrika, yayin gangamin yakin neman zaben jam’iyyar PDP na Jihar Ribas a karamar hukumar Okrika ta jihar.
Gwamnan ya ce abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun tabbatar da kalamansa na farko da ya yi a bainar jama’a cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da magoya bayansa suna takamar ba sa bukatar gwamnonin G-5 don shiga zaben 2023 da za a yi.
Wannan na zuwa bayan da gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi zargin da akwai wasu masu fada a ji a fadar shugaban kasa da ke yi wa Tinubu makarkashiya don faduwa zabe.
Sai dai Ministan Yada Labarai da Al’adu, Mista Lai Mohammed ya musanta wannan zargi, inda ya ce Buhari ba shi masaniyar wadanda ke son Tinubu ya fadi zabe.