Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Nnamdi Kanu, shugaban masu iƙirarin kafa ƙasar Biafra (IPOB), da ya fice daga kotun saboda halin da ya nuna na rashin ɗa a a gaban kotun.
Alkali James Omotosho ya yi watsi da sabbin buƙatu uku da Kanu ya gabatar bayan an ɗage shari’ar, yana mai cewa ba su da wani tasiri.
- Tsaro: Gwamnan Kano Ya Aike Mutane 1,600 Don Gadin Makarantu
- Dokar Fansho Ta Majalisar Dokoki: Dokar Son Kai Ko …?Kanun Labarai
Alƙalin ya kuma ce saboda “rashin ɗa a da kuma gatsali da Kanu ya ke nunawa a kotu, za a yanke masa hukunci ko da bai halarta zaman kotun ko kuma ya turo wakilansa ba”
Tun da farko, lokacin da Alƙalin ya yi ƙoƙarin yanke hukuncin, Kanu ya fara ɗaga murya da mayar da martani, yana mai cewa kotun ba za ta iya ci gaba ba saboda bai gabatar da hujjarsa ta ƙarshe a rubuce ba. Ya yi ta zargin cewa Alƙalin yana da son zuciya kuma bai fahimci doka ba.
Duk da haka, alƙalin ya ci gaba da yanke hukunci.














