Al-makura Ya Taimaka Wa Wadanda Ibtila’in Gobara Ya Shafa A Azare

Gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Almakura ya bayar da tallafin naira miliyan biyu (N2, 000,000) ga wadanda ibtila’in gobara shafa a kasuwar garin Azare da ke karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi watannin baya da suka gabata.

Gwamnan wanda ya aike da tawaga mai mutane uku zuwa jihar Bauchi a karkashin kwamishinan aiyuka na jihar Nasarawa, Injiniya Wada Yahaya, tawagar ta isa kai tsaye zuwa ga Sarkin Katagum Alhaji Umar Farouk II domin jajantawa hadi da miya kyautar, tawagar ta bayyana ibtila’in daga Allah madaukaki.

Tawagar sun gabatar da wasika mai lamba GHL/INF/1/BOL.BII/578 wanda gwamnan jihar ta Nasarawa ya sanya hanu da kansa, wasikar ta shaida cewar gwamnan ya ce ibtila’in ta auku ne a wani gabar da sai dai a nemi addu’ar samun sauki da kuma addu’ar kada hakan ta sake faruwa.

Daga bisani gwamnan ya jajanta ga illahirin ‘yan kasuwan da gobarar ta shafa, yana mai rokon Allah ya kiyaye sake aukuwar hakan a nan gaba.

Da yake amsar tallafin kudin, Sarkin Katagum Alhaji Umar Farouk ya gode wa gwamnan jihar Nasarawa a bisa agajin nasara, yana mai tabbatar da cewar kudaden za su taimaka wa wadanda lamarin ta shafa domin rage musu radadin asara.

Daga bisani ya shaida cewar Allah ya saka wa gwamnan da mafificiyar alkairi, kana Sarkin ya mika cikicin kudin ga kwamitin rage radadin gobarar babban kasuwar Azaren domin rabawa ga wadanda za su amfana da shi.

Har-ila-yau, sakataren babban kasuwar Azare na kwamitin kan gobarar, Saleh Mu’azu Azare ya rubuta wa gwamnan Nasarawar wasikar godiya mai kano kamar haka: ACMFDC/KEC/C/001/B.I inda yake tabbatar wa gwamnan kan cewar tallafin zai shiga hanun wadanda ya bayar dominsu, kana ya gode masa kan wannan kokarin nasa.

Idan za a iya tunawa dai, ita dai wannan gobarar wacce ta auku a ranar Lahadi 17th Yuni 2018, wacce ta shafe babban kasuwar Azaren gaba daya, inda aka yi asarar miyoyin naira da shaguna da manyan kadarori, tun bayan wannan lokacin ‘yan kasuwar suke samun tallafi daga wurare daban-daban a fadin kasar nan domin rage musu radadin wannan asarar da suka yi.

Exit mobile version