Daga Jamil Gulma,
NijarShugaban karamar hukumar mulki ta Dandi Honarabul Garba Salihu Dila (Gatan Kabi) ya bayyana cewa alakar al’ummar karamar hukumar mulki ta Dandi da kuma al’ummar jamhuriyar Nijar mai kyau ce musamman da yankin jihar Dosso da ya ke ita ce jiharda ta fi kusa da su.
Ya yi wannan bayanin ne a karshen makon da ya gabata sa’ilinda ya ke zantawa da wakilinmu a garin Kamba.
Honarabul Garba Dila ya ce kyakykywan zamantakewarmu da yan’uwanmu na jamhuriyar Nijar ta yi tasiri a zukatan mazauna wannan yankin wanda yana daga cikin abubuwan da suka haifarda zaman lafiya da muke da shi duk da ya ke akwai kabilu da yawa a wannan karamar hukuma da suka hada da hausawa, zabarmawa, fulani, kyangawa, dandawa da sauran baki da suka zo daga wadansu sassan kasarnan wajen kasuwanci saboda kasancewar ta kan iyaka.
Hakazalika a gwamnatance ma akwai ayuka na hadingwiwa da mu ke aiwatarwa tare musamman kan abinda ya shafi tsaro saboda a wannan lokacin shi ne ya fi zama barazana ga kasarnan, wannan hadingwiwa kuma ya inganta tsaro a wannan yankin sosai.
Daga karshe kuma Honarabul Garba Dila ya yi kira ga al’umma musamman mazauna cikin yankin karamar hukumar mulki ta Dandi da su guji duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiya da ke akwai musamman fulani makiyaya saboda gabadaya yanzu mutane sun fantsama wajen noman rani sanadiyyar ambaliyar da aka samu da ta mamaye amfanin gona a daminar da ta gabata.